Cibiyar lura da harkokin sadarwar intanet ta kasar Sin ko CNNIC a takaice, ta ce ya zuwa watan Yuni da ya gabata, adadin masu amfani da intanet a kasar Sin ya kai sama da mutane biliyan 1.12.
Rahoton da CNNIC ta fitar a Litinin din nan, ya nuna yadda sadarwar intanet ta karade kaso 79.7 bisa dari na sassan kasar ya zuwa watan na Yuni, adadin da ya karu da kaso 1.1 bisa dari kan na watan Disamban bara.
- Sin Ta Gina Tsarin Layin Dogo Da Manyan Hanyoyin Mota Da Na Aikewa Da Kunshin Sakwanni Mafi Girma A Duniya
- Rashford Na Dab Da Komawa Barcelona A Matsayin Aro
Kazalika, rahoton ya ce Sin ta yi matukar kokari wajen bunkasa fannin hidimar intanet, yayin da ake aiwatar da tsarin raya kasa na shekaru biyar-biyar karo na 14, wanda aka aiwatar tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025. A wannan fanni, an mayar da hankali matuka ga samar da hidimar intanet mai game daukacin al’umma, ciki har da rukunin tsofaffi, da mazauna karkara, domin raba gajiyar shirin da daukacin ‘yan kasar.
Rahoton ya kuma ce ya zuwa watan Yunin wannan shekara, Sin na da masu amfani da intanet ‘yan shekaru 60 ko fiye miliyan 161, da masu amfani da intanet dake zaune a yankunan karkara miliyan 322. Kuma kason masu amfani da intanet din a rukunonin biyu, ya kai kaso 52 bisa dari da kuma kaso 69.2 bisa dari.
A daya bangaren kuma, bunkasar hidimar intanet a kasar Sin ya taka muhimmiyar rawa wajen raya al’adun kasar a gida da waje, musamman idan an yi la’akari da yadda aka samu damar fitar da karin ayyukan adabi da wasannin intanet na Sin zuwa ketare, da ma yadda wasu bayanai da ake samu daga intanet din ke kara fito da tarin wuraren yawon shakatawa dake kasar ta Sin. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp