Jami’in hukumar lura da makamashi ta kasar Sin Zhang Xing, ya ce ya zuwa karshen watan Maris da ya gabata, adadin wuraren cajin ababen hawa masu aiki da sabbin makamashi da aka kakkafa a sassan kasar ya karu da kaso 47.6 bisa dari a shekara, a gabar da kasar ke ta fadada yawan cibiyoyin cajin ababen hawa masu aiki da sabbin makamashi ko NEVs.
Zhang, wanda ya bayyana hakan ga wani taron manema labarai da ya gabata a kwanan nan, ya ce ya zuwa karshen watan Maris, jimillar irin wadannan cibiyoyi na caji dake sassa daban daban na Sin sun kai miliyan 13.75. Ya ce, adadin ya hada da mallakin gwamnati miliyan 3.9, da na sassa masu zaman kansu miliyan 9.85.
Kazalika, akwai cibiyoyin cajin har 38,000 a manyan hanyoyin kasar, adadin da ya hade kaso 98 bisa dari na wuraren da ake ba da hidimomin kula da ababen hawa a fadin kasar, yayin da kuma yankuna masu matsayin lardi 13 dake kasar Sin suka cimma nasarar fadada samar da wuraren cajin zuwa dukkanin gundumomin dake karkashinsu, kuma da hakan an daga matsayin yawan cibiyoyin cajin a gundumomi zuwa kaso 76.91 bisa dari. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp