Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya bayyana cewa Adamawa na tare da Shugaba Bola Tinubu, inda ya kiran jama’ar jihar da su mara wa Tinubu baya.
Fintiri ya bayyana hakan ne yayin bikin miƙa motocin ƙungiyar PBAT Door-to-Door Movement ga masu gudanar da ayyukanta a jihar Adamawa.
An ƙaddamar da motocin ne domin ƙarfafa ayyukan ƙungiyar na wayar da kan jama’a da yaɗa manufofin Tinubu, tare da neman goyon bayan sake zaɓensa a 2027.
An ce motocin za su taimaka wajen kai saƙon ƙungiyar zuwa ƙananan hukumomi da yankuna a jihohi 14.
Da yake jawabi a wajen bikin, shugaban ƙungiyar na ƙasa, Sunday Adekanbi Asuku, ya buƙaci waɗanda suka amfana da motocin da su ƙara ƙaimi wajen hulɗa da jama’a da wayar da kansu game da manufofin ƙungiyar.
Asuku ya kuma yi kira ga masu gudanar da ayyukan ƙungiyar a jihohi da su ƙara ƙoƙari wajen neman goyon bayan sake zaɓen Tinubu.
Ƙungiyar ta ce za ta faɗaɗa ayyukanta zuwa wasu jihohi ta hanyar ƙara tuntuɓar jama’a ta hanyar neman shawarwari.














