Dan wasan gaba na Super Eagles, Ademola Lookman, ya samu nasarar lashe kyautar gwarzon dan wasan Afrika na shekarar 2024 da Hukumar Kwallon Ƙafa ta Afrika (CAF) ta bayar.
Bikin bayar da kyautar ya gudana a birnin Marrakech na Morocco, inda Lookman ya doke fitattun ‘yan wasa irinsu Simon Adingra daga Ivory Coast, Achraf Hakimi na Morocco, Serhou Guirassy daga Guinea, da mai tsaron gida Ronwen Williams na Afrika ta Kudu.
- Firaminista Li Qiang Ya Shugabanci Taron Majalisar Gudanarwar Kasar Sin
- Sin Ta Bayyana Matukar Adawa Da Aniyar Amurka Ta Sanya Karin Haraji Kan Wasu Hajojin Sin Dake Shiga Kasar
Lookman, wanda ke buga wasa a kungiyar Atalanta, ya haskaka sosai a bana.
Ya kafa tarihi a gasar Europa, inda ya zama dan wasa na farko tun shekarar 1975 da ya zura kwallaye uku cikin mintuna 26 a wasan ƙarshe.
Har ila yau, Lookman ya shiga jerin ‘yan wasa da suka yi takarar kyautar Ballon d’Or ta duniya a bana, inda ya zo na 14.
Sauran masu nasara a bikin sun hada da:
Ronwen Williams (Afrika ta Kudu): Gwarzon mai tsaron gida.
Lamine Camara (Senegal): Gwarzon matashin ɗan wasa.
Emerse Fae da tawagar Ivory Coast: Gwarzuwar kungiyar shekara.
A bangaren mata:
Barbra Banda (Zambia): Gwarzar ‘yar wasa.
Chiamaka Nnadozie (Nijeriya): Gwarzuwar mai tsaron gida.
Doha El Madani (Morocco): Gwarzar matashiyar ‘yar wasa.
Super Falcons (Nijeriya): Gwarzuwar tawagar mata ta Afrika.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp