Kawo yanzu dai an kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka da kasar Ibory Coast ta karbi bakunci kuma ta lashe gasar duk da rashin nasara da ta yi a wasanni biyu na cikin rukuni.
Abubuwa sun faru kafin da kuma bayan da tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta yi rashin nasara a wasan karshe tsakaninta da kasar Ibory Coast a yammacin ranar Lahadi, masana ke tsokaci dangane da dalilan da suka sanya Nijeriyar ta yi rashin nasara.
- Xi Ya Taya Stubb Murnar Zabarsa A Matsayin Shugaban Finland
- Gwamnonin PDP Sun Caccaki Gwamnatin Tarayya Kan Tsadar Rayuwa
Mai masaukin baki kasar Ibory Coast dai ta samu nasara a kan Nijeriya ne da ci 2-1 bayan Nijeriya ta fara zura kwallo a raga a miti na 38 bayan da dan wasanta, William Troost-Ekong ya sa wa kwallon kai yayin bugun kusurwa amma bayan dan wasan Ibory Coast, Franck Kessie ya farke kwallon, sannan kuma a minti na 82 Sebastian Haller ya kara kwallo ta biyu wadda da ita ce ta bai wa Ibory Coast nasara.
Annan nasara ta kasar Ibory Coast ita ce ta katse wa Nijeriyar mafarkinta na daukar kofin gasar ta AFCON a karo na hudu, tun bayan wanda ta dauka a shekarar 2013 a Afirka ta Kudu.
Amma akwai dalilai da suka janyo wa Nijeriya wannan rashin nasara wadanda nan gaba ya zama dole a dauki mataki a kansu domin gujewa irin wannan rashin nasara a wasan karshe.
Gano lagon Nijeriya: Da farko dai Nijeriya ta doke tawagar Ibory Coast a wasansu na cikin rukuni 1- 0, inda ‘yan kasar suka yi ta nuna rashin jin dadinsu a matsayinsu na masu masaukin baki har ta kai suka yi bore ciki har da kone-kone. Hakan ya sa kungiyar ta Elephants tsayawa ta yi karatun ta-nutsu domin karantar takun wasan ‘yan Super Eagles.
Kuma wannan gano lagon Nijeriya da ita Ibory Coast ta yi tabbas ya taimaka mata wajen samun nasara kan Nijeriya
Jin tsoron wasan: Bayan cin kwallo daya tilo da ‘yan Nijeriya suka yi a minti na 38 da fara wasa sai ‘yan wasan Super Eagles suka koma suka tare a bakin raga domin tsaron gida maimakon kokarin ganin sun kara jefa kwallaye kuma wannan mataki da ‘yan wasan suka dauka ya yi wa Nijeriya illa bisa la’akari da yadda ‘yan Ibory Coast din suka yi ta kai wa Nijeriya hare-hare iri-iri su kuma Super Eagles suka koma kariya kawai.
Matsalar ‘Yan wasan tsakiya: Nijeriya ta samu matsala a jerin ‘yan wasanta na tsakiya tun ba a je ko’ina ba inda ‘yan wasan suka koma kowa yana buga abin da ya ga dama da buge-buge ba tare da basira ba.
Amma shi kansa kociyan tawagar ta Super Eagles, Jose Peseiro bai boye gaskiya ba game da wannan rashin nasarar ta kungiyar da yake jagoranta inda a hirarsa da manema labarai ya ce lallai tawagarsa tana da kyau to amma a ranar Lahadin nan Ibory Coast sun koya musu yadda ake samun nasara.
Poseiro ya kuma amince cewa ‘yan Nijeriyar ba su samu yadda suke so ba domin sun rasa kwallaye da yawa kuma bai san mene ne ya sa hakan ba, ba na tsammanin ‘yan wasansa a nutse suke a ranar.
Ya kara da cewa ‘yan wasan sun bari an keta tsaron baya, sun rasa kwallaye da yawa ta haka ne suka bar abokan hamayya suka gano lagonsu suka kuma yi ta kai musu hare-hare.
Za a iya cewa kawo yanzu dai ba a san makomar Peseiro ba bayan kammala wannan gasar ta AFCON kuma da ma dai shugaban hukumar kwallon kafa ta Nijeriya, NFF Ibrahim Musa Gusau, a kwanakin baya ya ce sai bayan kammala gasar ne za su waiwayi yarjejeniyar da suka cimma da kocin na Nijeriya dan kasar Portugal.
Wadanne Kyaututtuka Aka Lashe A Gasar?
Kofi na uku ke nan da Ibory Coast ta lashe, bayan wanda ta ci a shekarar 1992 da kuma a 2015 kuma dan wasan Ibory Coast, Simon Adingra shi ne ya lashe kyautar wanda ya fi taka rawar gani a wasan karshe a AFCON ranar Lahadi.
Kyaftin din Nijeriya, William Troost-Ekong shi ne aka bai wa kyautar fitaccen dan wasan gasar baki dayan ta bayan ya zura kwallaye hudu a gasar kuma ya buga kowanne wasa har wasan karshe.
Dan wasan tawagar Ekuatorial Guinea, Emilio Nsue Lopez shi ne ya karbi kyautar takalmin zinare a matsayin wanda ya fi cin kwallaye bayan ya zura kwallaye guda biyar a raga.
Haka kuma mai tsaron ragar Afirka ta Kudu, Ronwen Williams shi ne mai tsaron ragar da babu kamarsa a gasar kofin Afirka da aka kammala a Ibory Coast kuma ya karbi kyautar ne bayan buge fenariti hudu a wasa da Cape Berde da kuma biyu a wasa da DR Congo ta kai Afirka ta Kudu ta kare a gurbi na uku.
Bayan da Afirka ta Kudu ta yi ta uku a AFCON a bana, ita ce ta karbi kyautar wasa ba da gaba ba da ake kira Fair Play saboda a lokacin bikin da aka yi ranar Lahadi, dan kwallon Togo, Emmanuel Adebayor ne ya fito da kofin Afirka filin wasa domin bai wa Ibory Coast.
Haka kuma Shugaban Kasa, Alassane Ouattara tare da shugan CAF, Dr Patrice Motsepe da na FIFA, Gianni Infantino ne suka mika kofin ga kyaftin din Ibory Coast, Mad Gradel.
Haka kuma an yi bikin bai wa hukumar kwallon kafar Morocco tuta da cewar ita ce za ta shirya wasannin da za a yi a shekarar 2025 kuma gasa ce ta 35 a tarihin gasar ta cin kofin Afirka.
Ga jerin wadanda suka lashe kyautuka a AFCON 2023 a Ibory Coast 2023
Wadda ta lashe kofin: Cote d’Iboire. Wadda ta yi ta biyu: Nijeriya. Wadda ta kammala a mataki na uku: Afirka ta Kudu. Wadda ta yi ta hudu: Jamhuriyar Dumukradiyyar Congo
Fitatcen dan wasan gasar: William Troost-Ekong (Nijeriya). Wanda ke kan gaba a cin kwallaye: Emilio Nsue Lopez. Fitatcen mai tsaron raga: Ronwen Williams (Afirka ta Kudu) Wasa ba da gaba ba: Afirka ta Kudu.