Wani hasashe da na’urar Opta tayi ya aza Nijeriya kan gaba a cikin jerin kasashen da suka fi damar lashe gasar AFCON ta bana da ake fafatawa a kasar Cote de’Voire.
Hakan ya faru ne bayan da aka fitar da manyan kasashe irinsu Senegal da Morocco daga gasar kamar yadda Opta supercomputer ta bayyana.
An bayyana Nijeriya a matsayin wadda keda kaso 28.8% na damar lashe kofin,inda take shirin karawa da Angola wasan kusa da na karshe a ranar Juma’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp