Yayin da ya rage ‘yan sa’o’i kadan a fafatawar da Super Eagles za ta yi da mai masaukin baki Cote d’Ivoire a rukunin (A) wasa na biyu, dan wasa mai buga baya, Bright Osayi-Samuel ya bayyana cewa, ya ci guba acikin abinci.
A cewar Soccernet.ng, tauraron Fenerbahçe, duk da cewa, yana fama da rashin lafiya amma yana da karfin gwiwa da kyautata zaton ingancin lafiyarsa a wasan da ake sa ran za a yi a ranar Alhamis.
- AFCON 2023: Morocco Ta Lallasa Tanzaniya Da Ci 3-0
- Kambun AFCON 2023: Babu Makawa Super Eagles Ta Doke Ivory Coast – Mikel Obi
“Na ci guba acikin abinci,” Osayi-Samuel ya tabbatar da hakan a wani gajeren bidiyo da Brila FM ta samu.
Osayi-Samuel dan wasa fitacce ne a bangaren tsaron baya ta gefen dama mafi aminci a tawagar Nijeriya a shekarar 2023, yana taka rawar gani sosai kuma ya ba da gudummawa ga nasarar da Nijeriya ta samu na shiga gasar AFCON 2023.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp