Kasar Tanzania ta kori mai horar da tawagar ‘yan wasan kasar da ke buga gasar kofin kasashen Afirika da ake ci gaba da gudanarwa a kasar Cote d’Voire.
Tanzania ta dakatar da kocinta Adel Amrouche bayan da hukumar kwallon kafar Afirka Caf ta dakatar da shi daga shiga harkokin kwallon kafa na tsawon wasanni takwas a kan wasu kalamai da ya furta bayan kammala wasan da Tanzania tayi rashin nasara a hannun kasar Maroko.
- Halin Da Wasu Jam’iyyun Siyasa Suka Tsinci Kansu
- Ya Sace Katan 20 Na Alkur’ani Da Hadisai A Kwara
An nada Amrouche a matsayin kocin Tanzania a watan Maris na 2023,inda ya jagorance su zuwa gasar Afcon bayan samun maki a wasansu da kasarsa ta haihuwa Aljeriya a wasansu na karshe na neman cancantar shiga gasar.