Kasar Afirka ta kudu ta sha alwashin karfafa alakar cinikayya tare da kasar Sin, karkashin dandalin baje kolin tsarin samar da kayayyaki na Sin ko CISCE, a gabar da wata babbar tawagar kasar ta shirya halartar baje kolin na CISCE dake tafe.
Wata sanarwa daga fadar gwamnatin Afirka ta kudu, ta ce mataimakin shugaban kasar Paul Mashatile ne zai jagoranci babbar tawagar kasar zuwa taron baje kolin, wanda zai gudana tsakanin nanakun 16 zuwa 20 ga watan nan na Yuli a birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin.
Sanarwar ta kara da cewa, babbar tawagar za ta kasance muhimmin jigo na ingiza cudanyar Afirka ta kudu da Sin, karkashin hadin gwiwar manyan tsare-tsare a sabon zamani. Kazalika, hakan zai karfafa matsayin Afirka ta kudu na kasancewa babbar cibiyar kasashen kudu da hamadar Sahara ta fuskar cinikayya, da zuba jari da hadin gwiwar raya masana’antu.
Bugu da kari, sanarwar ta ce ziyarar manyan jami’an za ta mayar da hankali ga gabatar da muhimman ayyukan dake bukatar juba jarin kamfanonin Sin, musamman bangaren sabbin yankunan raya tattalin arziki na musamman, da muhimman ababen more rayuwa, da bunkasa hadin kan sassan biyu, a fannonin cin gajiyar fasahohi masu tsafta, da bunkasa sana’o’in dijital, da daga matsayin masana’antu. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp