Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce nahiyar Afrika na da duk wata dama da albarkatun da ake buƙata domin ta samar wa kanta ci gaba, ba tare da dogaro da ƙasashen waje ba.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da takwaransa na Rwanda, Paul Kagame, a birnin Abu Dhabi na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
- Abubuwan Dake Kunshe Cikin Rahoton Shekara-Shekara Game Da Cinikin Shige Da Fice Na Kasar Sin
- Sin Za Ta Dauki Mataki A Kan Tankunkumin Fasahar AI Da Amurka Ta Kakaba
A cewarsa, lokaci ya yi da ƙasashen Afrika za su mayar da hankali kan ƙarfafa haɗin kai da kasuwanci a tsakaninsu domin al’ummar nahiyar su amfana.
Ya ƙara da cewa Afrika na da tarin albarkatun ƙasa, mutane masu ƙwazo, da ƙarfin da za ta iya tsayawa da ƙafarta.
Tinubu da Kagame suna Abu Dhabi ne domin halartar taro na mako guda kan ci gaba mai ɗorewa, wanda ake gudanarwa daga 12 zuwa 18 ga Janairu, 2025.
Sai dai, a halin yanzu, ƙasashen Afrika na fama da matsaloli irin su talauci da rashin haɗin kai, wanda hakan ya sa suke dogara kan taimakon ƙasashen duniya wajen samun ci gaba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp