Shugaban rukunin kamfanonin Dangote , Aliko Dangote, ya bayyana damuwa cewa nahiyar Afrika ta zama filin jibge man fetur mara inganci, sakamakon dogaro da shigo da man daga kasashen waje. Ya ce, banda Aljeriya da Libiya, mafi yawan ƙasashen Afrika na shigo da mai duk da yawan arziƙin ɗanyen mai da suke da shi.
A cewar Dangote, dalilin da ya sa ya kafa katafaren matatar mai shi ne domin Nijeriya ta samu ‘yancin kai a fannin sarrafa mai da kuma rage dogaro da ƙasashen waje. Ya ce matatar za ta kuma zama abin koyi ga sauran ƙasashen nahiyar wajen gina makamantan cibiyoyi da rage fitar da albarkatu ba tare da an sarrafa su ba.
Ya bayyana cewa da farko mutane da dama sun nuna shakku kan yiwuwar kammala aikin, har wasu na ba shi shawara ya janye. Sai dai ya ce sun nace da aikin ne saboda sun yarda da hangen nesa, duk da irin ƙalubalen da suka fuskanta. Ya ƙara da cewa ci gaban ƙasa ba zai yiwu ba tare da manyan ayyuka masu tasiri da kuma jarin cikin gida ba.
Dangote ya kuma roƙi attajirai ‘yan Nijeriya da su zuba jari a cikin gida, maimakon a fitar da kuɗaɗen su zuwa ƙasashen waje. Ya ce ko da a wasu ƙasashe akwai rashawa, amma akasari ana zuba kuɗaɗen cikin gida inda suke taimaka wa tattalin arziki, sabanin abin da ke faruwa a Afrika.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp