• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

AGOA: Tallafi ko Makami?

byCGTN Hausa
2 years ago
AGOA

A farkon wannan mako ne, shugaban Uganda Yoweri Museveni, ya soki matakin Amurka na cire kasarsa daga yarjejeniyar cinikayya ta AGOA, saboda abun da Amurka ta kira “take hakkokin bil adama”.

AGOA, yarjejeniya ce da Amurka ta gabatar a shekarar 2000 domin ba kasashen kudu da hamadar Sahara damar shigar da wasu kayayyaki sama da 1,800 cikin Amurkar ba tare da biyan haraji ba.

  • Kalaman Amurka Zai Iya Shafar Tattalin Arzikin Nijeriya – Minista
  • Bikin CIIE Ya Sa Kayayyakin Kasashen Afirka Samun Karbuwa

Sai dai, matakin Amurka ya sa alamar tambaya kan me taimakonta ke nufi: tallafi domin ci gaban kasashe ko kuma makamin tilasta musu akidunta? Matakin Amurka ya bayyana karara yadda take mayar da hankali wajen neman kakabawa kasashe masu tasowa ra’ayoyi da akidunta, ko da kuwa ba su dace da bukatu ko muradun wadancan kasashe ba. Amurka ta kan yi amfani da karfinta da tallafin da take ba kasashe masu karancin kudin shiga a matsayin wani makami na juya su yadda ta ga dama. Ta manta cewa, su ma ’yantattun kasashe ne dake da ikon cin gashin kansu da zartar da dokokin da suka dace da su.

Kasashen duniya sun bambanta da juna, al’adu ko addini ko kabila, ba za su taba zama iri daya ba. Kuma wannan bambancin shi ne ke kara kawata zaman rayuwa da koya mana yadda za mu zauna tare bisa girmamawa da hakuri da juna, kamar yadda shawarar kasar Sin ta wayewar kan duniya wato GCI ta gabatar, wato zaman jituwa da koyi da juna tsakanin mabanbanta al’ummomin duniya. Kowace kasa a duniya na da ikon zabarwa kanta dokokin da suka dace da ita. Uganda ta zabi zartar da dokar hana auren jinsi, abun da ya kamata Amurka ta yi shi ne, girmama zabin Uganda, da kaucewa tsoma baki cikin al’amuranta na ci gida. Cire sunan wasu kasashe da ta yi daga yarjejeniyar AGOA ya nuna cewa, ba ci gabansu take nema ba kamar yadda take ikirari, cin zali da yadda za ta kasance mai babakere a duniya, shi ne burinta.

Amurka ta kan zartar da dokoki ko aiwatar da ayyuka, amma wadannan kasashe ba sa tsoma baki cikin al’amuranta, maimakon ta girmama ’yancinsu kamar yadda suke girmama ta, sai take amfani da karfinta wajen danniya da cin zali. A lokaci guda kuma, take ganin laifinsu da neman haddasa fitina a dangantakarsu da kasar Sin.

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Sharadin huldar kasar Sin da kasashen ketare shi ne girmama juna da girmama cikakken ’yancin kasashe da moriyar juna ba tare da sharadi ba da kauracewa tsoma baki ko katsalandan cikin harkokinsu na gida, lamarin da ya sa take samun karbuwa a tsakanin kasashen duniya musamman masu tasowa.

Ya zama wajibi Amurka ta sake nazari ta sauya takunta domin kasancewarta daya tilo mai karfi a duniya, ba abu ne da zai yiwu ba, kana matakai maras dacewa da take dauka, suna kara rage kimarta a idon duniya.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
IMF: GDPn Sin Zai Karu Da Kashi 5.4 A Shekarar 2023

IMF: GDPn Sin Zai Karu Da Kashi 5.4 A Shekarar 2023

LABARAI MASU NASABA

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Go to mobile version