Wasan da kungiyar Kano Pillars FC ta buga da Shooting Stars (3SC) ta Ibadan a gasar firimiya ta Nijeriya ya bar baya da kura bayan da 3SC ta zura kwallo a ragar Pillars a mintunan karshe na wasan, hakan ya janyo tashin hankali tsakanin magoya bayan Pillars din da yan wasan 3SC.
Wasan wanda aka buga ranar Lahadi 12 ga watan Oktoba, 2025, a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano, ya kare ne da ci 1-1 inda Shooting Stars ta ci kwallonta a minti na 94, hotunan bidiyo da ke yawo a yanar gizo sun nuna yadda magoya bayan kungiyar Kano Pillars suka harzuka har wasunsu na dukan yan wasan Shooting Stars da jami’an wasa a fadin filin wasan yayin da suke ta kokarin tsira da lafiyarsu.
Da ta ke mayar da martani kan lamarin, kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta fitar da wata sanarwa inda ta yi Allah-wadai da rashin da’a da wasu mutane suka nuna a wasan, yayinda kuma suka yabawa jami’an tsaro da suka yi gaggawar shiga tsakani, a cewar sanarwar mai dauke da sa hannun jami’in yada labarai na kungiyar, Abubakar Isa Dandago, wasu bata-gari ne suka haddasa matsalar bayan kammala wasan, amma jami’an tsaro da masu kula da filin wasan suka shiga tsakani da wuri.
Sanarwar ta kara da cewa, “mun yi farin cikin ganin cewar yan wasan kungiyoyin biyu da jami’an wasan duk sun bar filin wasan ba tare da samun wani rauni ba kuma jami’an tsaro suka yi musu rakiya, kungiyar ta kara da cewa an kama wasu da dama da ake zargi da hannu a rikicin tare da mika su ga hukumomin tsaro domin gudanar da bincike tare da gurfanar da su gaban kuliya.
Kungiyar ta jaddada kudirinta na tabbatar da zaman lafiya da da’a, kungiyar ta jaddada cewa za ta ci gaba da tabbatar da ingancin wasan kamar yadda hukumar NPFL da hukumar kwallon kafar Najeriya NFF ta tanada, Pillars ta kuma yi kira ga magoya bayanta da su gudanar da ayyukansu cikin lumana tare da ci gaba da ba kungiyar goyon baya, amma kuma wani bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta ya nuna yan wasan 3SC da aka jikkata tareda raunuka a jikinsu.