Alhazan Najeriya 7,582 ne aka yi jigilarsu zuwa Madina ta ƙasar Saudiyya a matakin farko na aikin Hajjin bana. Tashin jiragen wanda ya fara kwanaki biyar da suka gabata a filin jirgin saman Sir. Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi, mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima ne ya ƙaddamar da jirgin farko na maniyyatan.
Tashin jirgin Air Peace mai ɗauke da alhazan birnin tarayya 311 da kuma jirgin Flynas mai alhazan Kebbi 431 shi ya kawo adadin alhazan Najeriya 7,582 da suka isa Saudiyya. An yi jigilar waɗannan alhazai ne a cikin jirage 18.
- Hajjin Bana: Nijeriya Ba Za Ta Yi Amfani Da Sararin Samaniyar Sudan Ba – NAHCON
- Hajjin 2024: Ranar 10 Ga Watan Yuni Za A Kammala Jigilar Maniyyata – NAHCON
Ƙididdigar NAHCON ta tabbatar da cewa kawo yanzu jirgin MAX AIR ya yi jigilar maniyyata 2,966 daga jihohin Nasarawa, da Bauchi, da Oyo a jirage shida. Jirgin Flynas ya yi jigilar maniyyata 3,395 daga jihohin Kebbi, da Legas, da Ogun a cikin jirage bakwai, yayin da jirgin Air Peace ya yi jigilar maniyyatan FCT 910 daga filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe.
A yau ne Alhazan Nijeriyar da ke Madina za su fara tashi daga Makkah bayan sun shafe kwanaki huɗu a birni na biyu mafi tsarki ga Musulmai inda suka kammala zangon farko na aikin Hajjinsu.