Kungiyar masana’antar kwal ta Sin ta bayar da rahoton yawan hakar kwal a farkon rabin bana, inda alkaluma suka nuna cewa, manyan masana’antu sun samar da kwal tan biliyan 2.4, wanda ya karu da kashi 5.4% idan aka kwatanta da na makamancin lokacin shekarar da ta gabata.
Haka kuma cikin watanni shidan farko na bana, an gudanar da aikin samar da wutar lantarki mai aiki da kwal yadda ya kamata.
Bugu da kari, yawan kwal da aka shigo daga ketare ya kai tan miliyan 222 a rabin farkon bana, wanda ya ragu da kashi 11.1%.
Rahoton ya kuma bayyana cewa, an kammala gina masana’antun hakar kwal masu amfani da fasahohi na zamani 907, kuma yawan kwal da aka haka ta hanyar amfani da su ya fara wuce 50% a karon farko. Matakin ya maye guraben aikin yi masu hadari matuka sama da 16,000 , wanda ke nuna cewa aikin hakar kwal ya shiga wani sabon mataki na aminci da inganci. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp