Ma Zhaoxu, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin, ya bayyana a yau Alhamis, a wajen wani taron manema labaru da ya gudana cikin cibiyar kafofin watsa labarai ta taron wakilan jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 20 cewa, aikin hulda da kasashen ketare na kasar Sin ya samu ci gaba matuka, cikin shekaru 10 da suka wuce, inda yawan kasashen da ta kulla huldar diflomasiyya da su ya karu daga 172 zuwa 181.
Jami’in ya nanata babban makasudin aikin hulda da kasashen waje na kasar Sin, wato kokarin kare zaman lafiya a duniya, da neman samun ci gaba tare da sauran kasashe, don kafa wata al’ummar dan Adam mai kyakkyawar makoma ta bai daya.
Ban da wannan kuma jami’in Sin ya ce, kasarsa na adawa da matakan saka wa wasu kasashe takunkumi bisa ra’ayi na kashin kai, da matsawa sauran kasashe lamba don tilasta musu bin umarni, kana sam ba za ta yarda ba, da yadda wasu bangarorin ke neman tsoma baki cikin harkokin gidan Sin, ta hanyar fakewa da batun kare hakkin dan Adam. (Bello Wang)