Sarkin Kasuwar Katagum, Alhaji Musa Bello ya bayyana cewa aikin katafariyar gadar da ake yi a unguwar Hotoro NNPC da ke Jihar Kano, wacce Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje yake ginawa har ya sanya mata suna Muhammadu Buhari ci gaban Nijeriya ce gaba daya.
Ya kara da cewa wannan aikin gada zai amfani Nijeriya ne baki daya ba Jihar Kano ba kadai, bisa la’akari da yadda gadar ta hada hanyoyi na shugowa Kano daga sassa daban-daban na Nijeriya.
Shugaban Kasuwar Katagum ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wuri wani taro da ya gudana a ranar Laraba da ta gabata a Jihar Kano.
A cewarsa, idan aka yi la’akari da wannan aiki na Gwamna Ganduje ya kawo wa Kano ci gaba mai yawa, dan haka wannan aiki abun a yaba wa Gwamnatin Jihar Kano ne kan wannan aiki. Haka kuma ya yaba wa gwamnatin tarayya kan ayyukan titin da ta ke yi a kokarinta na bunkasa sufuri a Nijeriya.
Alhaji Musa Bello ya bukaci gwamnatin da ta dukofa wajen gyara hanyoyi da suka lalace, musammam irin hanyar Makwa da ke Jihar Neja da dai sauran manyan hanyoyi da suke bukatar kulawa daga gwamnati, Saboda mahimanci su ga al’umar Nijeriya.