Jakar madaciya na nan danfare da hanta, daga kasan hantar a bangaren dama daga sama a cikin Dan’adam.
Hanta ce ke samar da ruwan madaciya, wadda ke da launin kore ko kuma rawayar gwal, sannan sai ruwan madaciyar ya gangaro zuwa cikin jakar madaciya; domin ajiya zuwa lokacin da za a bukace shi.
- Dalilai 15 Na Muhimmancin Tsara Yadda Malami Zai Koyar Da Darussa A Aji (2)
- Yan Bindiga Sun Kashe Mutum Ɗaya Tare Da Ƙona Gidaje A Gombe
Kazalika, Hanta na iya samar da ruwan madaciya da yawansa ya kai kimanin lita 800 zuwa 1200 a kullum. A yayin da jakar madaciyar ke iya cin ruwan madaciyar da yawansa ya kai lita 50 bayan ta tace mafi yawan ruwan da ke ciki.
Har ila yau, ruwan madaciya ya kunshi kashi 97.6 cikin 100 ruwa zalla da kuma kashi 2.4 cikin 100 na gishirin madaciya da sauran burbishin ma’adanai da sauran makamantansu.
Gishirin madaciya shi ne jigon aikin madaciya a jikin Dan’adam, musamman wajen narka abinci da mutum ya ci.
Haka zalika, gishirin madaciya shi ne jigon sinadarin da ke narka ko markada abinci a ajin mai ko kitse a cikin karamin hanji, har a mayar da shi zuwa yadda jiki zai iya zukar sa daga karamin hanji zuwa sassan jiki.
Bugu da kari, gishirin madaciya na taimakawa wajen yi wa hanta kaimi; don samar da ruwan madaciya a jikin mutum.
Har wa yau, gishirin madaciya na taimakawa wajen saukaka fitowar bayan-gida daga cikin babban hanji zuwa dubura. Haka kuma, daga cikin ruwan madaciyar ne bayan-gida ke samun launi irin na ruwan kasar da yake da shi.
Tsakuwar madaciya: A yayin da kwalastirol ko kitse ya yi yawa a jikin mutum, kwalastirol din na iya curewa wuri guda ya haifar da matsalar da ake cewa; tsakuwar madaciya wato ‘gallstone’ a turance. Gishirin madaciya na taimakawa wajen magance curewar kwalastirol a cikin jakar madaciyar da ke jikin Dan’adam.
Haka zalika, duk da dimbin alfanun da madaciya ked a shi a jikin Dan’adam, ana iya yin tiyata a cire jakar madaciyar idan aka samu matsalar tsakuwar madaciya; sannan kuma a gaza samun magungunan da za su magance cutar tsakuwar.