A wani sabon rahoto da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta fitar, ya nuna cewa; fannin aikin noma a zango na hudu a 2024, ya sauka; musamman idan aka kwatanta da wanda aka samu a 2023.
Sai dai, a cewar wata kididdiga kan tattalin arzikin kasa da aka fitar a ranar Talata ta nun cewa; fannin aikin noma na kasar, ya samu karin kimanin kashi 1.17 a zango na hudu.
- Matsalar Wuta Ta Jefa Wasu Sassan Nijeriya Cikin Duhu
- Xi Ya Yi Kira Da A Kammala Tsare-Tsaren Bunkasa Rundunar Sojin Kasar Sin Na Shekaru 5 Cikin Nasara
Wannan sabon rahoto da Hukumar ta fitar, ya nuna cewa; fannin aikin noman, ya karu da kashi 1.17, inda wannan karuwar ta nuna cewa, ta dara da kashi 1.14 da aka samu a zango na uku na shekarar 2024.
Kazalika, wannan karuwa da aka samu a zangon na hudun, ta dara wadda aka samu a zango na hudun shekarar 2023, inda aka samu kashi 2.10.
Bugu da kari, rahoton ya nuna cewa; an samu karin da ya kai kashi 1.19 a zango na hudu na 2024, idan aka kwatanta da kashi 1.13 da aka samu a 2023.
Wasu kwararru a fannin na aikin noman, sun alakanta samun wannan karuwar, saboda dauki daban-daban da gwamnatin tarayya ta samar ga fannin, musamman wajen kokarinta na rage kalubalen rashin tsaro.
Daga cikin wannan daukin na gwamnati, sun hada da kirkiro da shirin jami’an tsaro na sintiri sama da 1,000 da aka tura zuwa kanannan hukumomi 19 a 2024, don bai wa manoma da amfanin noma da aka shuka kariya, inda shirin ya taimaka wajen kara bunkasa aikin noma.
A cewar Hukumar ta ‘NBS’, fannin aikin noma ya samar da kashi 25.59 wajen habaka fannin tattalin arzikin kasar, wato ma’ana, a zango na uku na 2023, gudunmawar da fannin ya samar ga tattalin arzikin kasar, ya tsaya ne a kashi 26.11, idan aka kwatanta da gudunmawar da fannin ya samar ga tattalin arzikin kasar a 2024, wacce ta kai kashi 26.11.
Fannin aikin noman kasar, ya ci gaba da kasancewa kan gaba, musamman a bangaren day a shafi tattalin arzikin Nijeriya, duba da yadda daukacin fannin ya samar karuwar da ta kai kashi 90.70 cikin 100.
Haka zalika, a 2023, an samu raguwa da kshi biyu tare kuma da samun wata raguwar da ta kai kashi 3.86 a zango na hudu na 2023.
Daga shekara zuwa shekara, tattalin arzikin Nijeriya ya karu da kashi 3.84, wato a zango na hudu na 2024, wanda ya dara da kasshi 3.46 da aka samu a 2023.
“Kokarin da aka samu a fannin habaka tattalin arzikin kasar a zango na hudu na 2024, ya samu ne saboda garanbawul da aka yi wa fannin, inda aka samu karuwar da ta kai kashi 5.37, wanda hakan ya kara tallafawa fannin bunkasa tattalin arzikin kasar”, in ji rahoton.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp