• English
  • Business News
Monday, October 20, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Ainihin Ma’anar Farfado Da Kasar Sin A Sabon Zamani

by CMG Hausa
3 years ago
Kasar Sin

Ga duk mai bibiyar yadda babban taron wakilan JKS na 20 ke gudana, ba zai gaza jin jimlar “farfado da kasar Sin daga dukkanin fannoni a sabon zamani da ake ciki” ba, musamman cikin rahoton da shugaban kasar, kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping ya gabatar, wanda hakan buri ne na raya kasar da JKS ta sha alwashin cimmawa.

A karkashin wannan manufa, akwai muhimman matakai masu dacewa da salon gurguzu mai sigar musamman da kasar Sin ke bi, wanda ya tanadi samarwa al’ummar Sinawa yanayin rayuwa mai cike da zaman lafiya da wadata, da zamanantar da tattalin arziki da zamantakewa, da bunkasa al’adu, da kyautata alakar rayuwa tsakanin bil adama da sauran halittu, wadanda sakamakon su zai amfani dukkanin sassan alummun kasar ba wai wasu mutane kalilan ba.

  • Tsarin Zamanintar Da Aikin Noma Na Sin Ya Gaggauta Bunkasuwarta Da Ma Duniya Baiki Daya

Idan muka kalli wannan salon samar da ci gaba na kasar Sin, za mu ga ya sha banban da na kasashen yamma masu bin salon jari-hujja, wadanda tarihi ya jima da sanin su, a matsayin masu amfani da karfin tuwo, da mulkin mallaka wajen fadada tasirinsu a duniya, da cimma muradun kashin kai ta kowace irin hanya.

Ko shakka babu, salon gurguzu mai halayyar musamman na Sin, ya haifar da babbar dama ta yakar talauci, inda karkashinsa kasar ta cimma nasarar tsamo al’ummarta da yawansu ya kusa miliyan 100 daga kangin talauci cikin shekaru 10 kacal, matakin da masu fashin baki ke ganin ya shiga tarihin duniya, a matsayin irin wanda ba a taba gani ba a shekarun baya bayan nan.

Alal hakika, JKS ta dora muhimmancin gaske ga moriyar al’ummar Sinawa. Jam’iyya ce da har kullum ke aiki tukuru, wajen ganin ba a bar wani rukuni na al’umma a baya ba a dukkanin fannonin ci gaba.

LABARAI MASU NASABA

Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20

Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin

Ana kuma iya ganin hakan a zahiri, idan aka yi duba ga bangarorin da kasar Sin ta cimma manyan nasarori a cikinsu, kamar bunkasar tattalin arziki, da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da fadadar fannin ilimin kimiyya da fasaha, da karuwar guraben ayyukan yi, da tsara manufofin inganta rayuwar tsofaffi da yara kanana da sauran su.

Tabbas wannan kadan ne daga ainihin ma’anar matakan farfado da kasar Sin a sabon zamani.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20

October 19, 2025
Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin
Daga Birnin Sin

Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin

October 19, 2025
Tie Ning Ta Halarci Bikin Bude Taron Karawa Juna Sani Na ‘Yan Majalisun Dokokin Kasashen Afirka
Daga Birnin Sin

Tie Ning Ta Halarci Bikin Bude Taron Karawa Juna Sani Na ‘Yan Majalisun Dokokin Kasashen Afirka

October 19, 2025
Next Post
Kasar Sin Ba Za Ta Sauya Niyyarta Ta Habaka Bude Kofa Ga Kasashen Waje Ba

Kasar Sin Ba Za Ta Sauya Niyyarta Ta Habaka Bude Kofa Ga Kasashen Waje Ba

LABARAI MASU NASABA

Bayan Kauce Hanya, Jirgi Ya Afka Cikin Teku A Hong Kong 

Bayan Kauce Hanya, Jirgi Ya Afka Cikin Teku A Hong Kong 

October 20, 2025
Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow A Abuja

Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow A Abuja

October 20, 2025
Wani Mai Taɓin Hankali Ya Kashe Mutum 1, Ya Raunata 3 A Taraba

Wani Mai Taɓin Hankali Ya Kashe Mutum 1, Ya Raunata 3 A Taraba

October 20, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

‘Yansanda Sun Kama Alburusai 400 A Delta

October 20, 2025
Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin Gamuwarsu

Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin Gamuwarsu

October 19, 2025
Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20

Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20

October 19, 2025
Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC

Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC

October 19, 2025
Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin

Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin

October 19, 2025
Ɗan Jarida Ibrahim Ɗan’uwa Rano Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Tsare Shi

Ɗan Jarida Ibrahim Ɗan’uwa Rano Ya Shaƙi Iskar Ƴanci Bayan Tsare Shi

October 19, 2025
Tie Ning Ta Halarci Bikin Bude Taron Karawa Juna Sani Na ‘Yan Majalisun Dokokin Kasashen Afirka

Tie Ning Ta Halarci Bikin Bude Taron Karawa Juna Sani Na ‘Yan Majalisun Dokokin Kasashen Afirka

October 19, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.