Wata ƙungiya mai zaman kanta da ke wayar da kan al’ummar Arewacin Nijeriya kan muhimmancin yin zabe, cusa da’a, nuna kishin kasa da kyautata tarbiyya mai suna ‘Adbocacy for Integrity and Rule of Law Initiatibe’ (AIRLIN) ta yi kira ga ’yan Nijeriya, musamman mazauna yankin Arewa da su shiga cikin harkokin zabe ta hanyar amfani da ’yancin da tsarin mulki ya ba su da kuma zaben shugabanni nagari.
Shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Muhammad Ibrahim Gamawa ne ya yi wannan kiran a yayin bikin kaddamar da shugabannin jiha da kananan hukumomin Jihar Kaduna a Arewa House, ranar Talata.
- 2027: Babu Dan Takarar Da Zai Iya Cin Zabe Ba Tare Da Goyon Bayan Arewa Ba – Baba Ahmed
- An Gano Cushen Biliyan 5 Cikin Kasafin Kuɗin Hukumar Alhazai Ta Ƙasa
Gamawa ya jaddada cewa, manufar kungiyar tasu ita ce a bai wa ’yan Nijeriya shawarar su kasance masu bin doka da oda, da mutunta juna ba tare da la’akari da bambancin addini da al’adu ba, yana mai cewa, kare martaba Nijeriya aiki ne da ya rataya a wuyan ’yan kasa, a ciki da wajen Nijeriya.
“Don haka ne ma muka zo nan domin aaddamar da daya daga cikin ofisoshi 15 da muke da su a jihohin Arewa 19, domin burinmu shi ne mu mamaye dukkan jihohin Arewa, mun zo ne domin mu yi kira ga ‘yan kasa su zo su kada auri’a a cibiyar da za su zabi shugabanni nagari.
“Idan za a iya tunawa a zaben da ya gabata, kashi 42 cikin 100 na masu kada kuri’a ne kawai suka halarci wurarren zabe, 68 kuma ba su halarta ba wanda hakan ba shi da kyau ga kasar nan, don haka dole ne mu fito mu san wadanda suka kasa zabe, mu fahimtar da su su zabi shugabanni da suka dace.
A wani bangare na manufofinsu na kara yawan masu kada kuri’a, Alhaji Gamawa ya bayyana cewa, kungiyar mai zaman kanta za ta taimaka wa ‘yan kasa wajen karbar katin zabe, “Lokacin da INEC ta bude dandalin rajistar katin zabe, za mu taimaka musu wajen karbar katin zabe domin su bada gudunmawa a zabe da kuma amfani da ’yancinsu.
Gamawa ya kuma yi magana kan muhimmancin samun katin shaidar zama dan kasa, inda ya ce, yayin da tsaro ya yi karanci, abu ne mai sauki a laka wa dan Nijeriyar ba shi da katin dan kasa sharrin zama bako ko dan mamaya ko kuma sanya shi cikin masu garkuwa da mutane.
“Rashin katin shaidar zama dan kasa babbar matsala ce ga ’yan Nijeriya musamman wadanda ke zuwa yankin Kudancin kasar nan.
“Amotekun ko wasu kungiyoyin al’adu ne za su tare su, za a tattara su a ce su bayyana kansu da kuma inda suka fito, wasu ma suna zargin su ba ’yan Nijeriya ba ne.
“Wasu za su ce ‘yan Kaduna ne amma ina katin shaida? Babu wata shaida ko da ta lasisin tuki ce.”
Ya kuma bayyana cewa, kungiyarsa na shirin gudanar da wani taro na kwana daya domin karbar bakuncin Malamai akalla 200 a karamar hukumar Gamawa wadanda za su zo a wayar da kan jama’a game da gina kasa da hakkokin ‘yan kasa da ayyukansu sannan kuma su wayar da kan dalibai da ke karkashinsu.
A nasa jawabin, shugaban AIRLIN na Jihar Kaduna Alhaji Musa Muhammed ya ce, kungiyar ta dukufa wajen ganin ta kawo sauyi mai kyau da zai dawo da martaba da mutunta ‘yan Nijeriya.
Ya kara da cewa, AIRLIN gida ce ga kowa da kowa musamman wadanda suka yi imanin cewa akwai bukatar a sake farfado al’amuran da suka rushe a Nijeriya.
Taron dai ya samu halartar dukkan shugabannin kungiyar na jiha da na kananan hukumomin jihar, tare da ‘yan rakiyar shugaban na kasa da suka taho
daga Abuja.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp