Wasu mazauna ƙauyen Zalla Bango a ƙaramar hukumar Sabon Birni, Jihar Sokoto, sun rasa rayukansu a wani haɗarin jirgin ruwa yayin da suke tserewa daga harin ƴan bindiga. Lamarin ya faru ne da yammacin Alhamis, 18 ga Satumba, lokacin da Kwale-Kwalen da ke ɗauke da jama’a yayi karo da dirkar gadar ruwa da ta rushe a kan hanyar Goronyo–Sabon Birni, hakan ya haddasa fashewarsa sannan ya nutse.
Shaidu sun bayyana cewa mafi yawan waɗanda abin ya rutsa da su mata ne da suka hau jirgin cikin gaggawa don tsallaka ruwa, su kuɓuta daga harin da ake tsammani an kai musu. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da jama’a ke ci gaba da barin gidajensu saboda hare-haren ƴan bindiga masu yawa a yankin.
- Gwamnatin Sokoto Ta Ƙaryata Rahoton NBS Kan Talauci, Ta Ƙaddamar Da Sabon Bincike
- Gwamnatin Sokoto Ta Ƙaryata Rahoton NBS Kan Talauci, Ta Ƙaddamar Da Sabon Bincike
Shugaban ƙaramar hukumar Sabon Birni, Alhaji Ayuba Hashimu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce adadin waɗanda suka mutu har yanzu ana bincike, sai dai an samu gawar mace guda ɗaya. Ya bayyana cewa jami’ai suna ci gaba da aikin ceto da neman sauran waɗanda suka bace.
Lamarin ya ƙara nuna irin mummunan tasirin rashin tsaro a Sokoto ta Gabas. A kwanakin baya ma, mutane shida sun mutu a Garin Faji bayan jirgin ruwa ya kife yayin da suke gudun harin ƴan ta’adda, yayin da ƴan bindiga kuma suka kashe wasu shida a Kwanar Kimba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp