An rantsar da tsohon ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Simon Lalong a matsayin Sanata mai wakiltar Filato ta Kudu a majalisar wakilai ta 10.
Lalong wanda ya samu rakiyar shugaban jam’iyyar APC na kasa yayin rantsar da da shi da misalin karfe 11:57 na safe a yayin zaman majalisar da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya jagoranta.
- Muna Roƙon Tinubu Da Ya Sake Naɗa Ministan Da Zai Maye Gurbin Lalong Daga Filato Ta Tsakiya – Komsol
- Lallai A Rika Hukunta Masu Aikata Laifukan Zabe
Tafiyar Lalong zuwa majalisar dattijai ta biyo bayan hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na tabbatar da shi a matsayin sanata.
Tunda farko dai hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta bayyana, Napoleon Bali, dan takarar jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 148,844 yayin da Lalong ya samu kuri’u 91,674 a zaben.
Da yake kalubalantar nasarar da Bali ya samu, Lalong ya garzaya kotun, yana mai cewa PDP ba ta da tsarin da ya dace wurin tsayar da dan takararta ba.
A hukunci da mai shari’a Muhammad Tukur ya yanke, kotun ta soke nasarar da Bali ya samu da kuri’un da dan takarar PDPn ya samu a zaben.
Bali ya daukaka kara zuwa kotun daukaka kara, karkashin jagorancin mai shari’a Elfrieda Williams-Dawodu. Duk da zanga-zangar da PDP ta yi, kotun daukaka kara ta sake tabbatar da Lalong a matsayin halastaccen Sanatan yankin.