• English
  • Business News
Tuesday, October 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Akwai Alamar Tambaya A Sake Lalacewar Matatar Mai Ta Fatakwal A Karo Na 2, Bayan Kashe Dala Biliyan 1.5

by Abubakar Sulaiman
5 months ago
Fatakwal

Bayan an sake rufe matatar man fetur ta Fatakwal a cikin watanni biyar, mutane da dama a Nijeriya, ciki har da Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya (NLC), Ƙungiyoyin farar hula (CSOs), da kuma masana a fannin mai, sun yi kira ga waɗanda ke kula da wannan kamfani na gwamnati su yi bayani.

A watan Disamba na shekarar 2024, wata jarida ta ruwaito cewa masana’antar ta daina aiki bayan ba a daɗe da ta fara samar da kayayyaki ba. Rahoton ya nuna cewa an daina fitar da man fetur a ranar Juma’a, 13 ga Disamba, inda duk wuraren shigar da man fetur a sabuwar masana’antar suka kasance babu kowa.

LEADERSHIP ta na sane cewa kusan wata guda kafin haka, a ranar Talata, 26 ga Nuwamba, 2024, tsohon shugaban kamfanin Mai na Nijeriya (NNPCL), Mele Kyari, ya ƙaddamar da wannan masana’antar mai samar da ganga 60,000 a kowace rana, inda mutane suka yi farin ciki da hakan. Amma yanzu, sake rufe masana’antar don gyare-gyare ya haifar da tambayoyi game da yadda gwamnati ke sarrafa matatun man fetur na ƙasar.

Masana da masu sharhi a fannin shari’a sun nuna rashin gamsuwa a cikin gudanar da ayyukan masana’antun. Kamar yadda LEADERSHIP ta fahimta, akwai babban giɓi a aikin sa ido da ya kamata hukumar kula da masana’antar ta yi. Taiwo Ogunloye, wani masani a fannin makamashi kuma lauya mai ilimin fasaha, ya shaida wa wakilinmu cewa rashin bayar da rahoton bincike game da masana’antun daga hukumar kula da harkokin Mai ta Nijeriya (NMDPRA) ya haifar da shakku game da gudanar da su.

Ogunloye ya ce, sashi na 32 na Dokar Masana’antar Mai (PIA) ya bai wa hukumar ikon yin bincike kan matatun da kuma bayar da ƙa’idojin aiki. Ya ƙara da cewa rashin sa hannun hukumar ya ɗora nauyi kan NNPCL, saboda jama’a ba su san halin da matatun ke ciki ba. Ya kuma nuna damuwarsa game da rashin bayyana ainihin dalilin rufewar waɗannan matatun mai da gwamnati ta kashe kuɗaɗe masu yawa wajen gyarawa.

LABARAI MASU NASABA

Majalisar Dattawa Ta Maido Da Ranar Tantance Sabbin Shugabannin Sojoji Zuwa Laraba

An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

“Ina ganin ya kamata NNPCL ta bayyana matsalolin da ke tattare da masana’antun, ta kuma nuna musamman waɗanne sassa suka shafa, domin mutane su iya tantance ingancin gudanar da su,” in ji shi. Eche Idoko, kakakin Kungiyar masu tace man Fetur ta Nijeriya (CORAN), shi ma ya kuka game da zargin rashin gaskiya, yana mai cewa jama’a ba su da masaniya game da yanayin da masana’antar take ciki.

Idoko ya yi kira da a sake bincikar kuɗaɗen da gwamnati ta kashe wajen gyara masana’antar NNPCL. A cewarsa, duk da tallafin gwamnati, farashin kayayyakin da masana’antar ta NNPCL ke fitarwa ya fi na masana’antar Dangote tsada. Ya ce CORAN ta kasance tana neman a ba da dama ɗaya ga duk masu haƙo man fetur, kuma ya yi kira da gwamnati ta ba da tallafi ga sauran masu tace man fetur masu zaman kansu.

A wani ɓangaren, Henry Adigun, mai sharhi kan harkokin yau da kullum kuma masani a fannin makamashi, ya ce bai kamata a ɗauki gyaran da NNPCL ta yi na yau da kullum ba a matsayin abin mamaki. Ya bayyana cewa, tun da matatar ta daɗe tana hutun aiki, to ana sa ran za a gano matsaloli bayan gyara, kuma za a gyara su yayin da suke tasowa. “Ya kamata mu fahimci cewa tsohuwar masana’anta ce, ba sabuwa ba, don haka ya kamata a yi gyare-gyaren da suka dace,” in ji shi.

LEADERSHIP ta ruwaito cewa NNPCL ta sanar da rufewa masana’antar Fatakwal don gyara tun daga ranar 24 ga Mayu. A cewar Femi Shoneye, Babban Jami’in Sadarwa na kamfanin, za a yi wannan gyaran na tsawon wata guda, kuma kamfanin yana aiki tare da masu ruwa da tsaki don tabbatar da inganci da gaskiya. “Muna aiki tare da duk masu ruwa da tsaki, ciki har da hukumar kula da harkokin Mai ta Nijeriya, don tabbatar da cewa an yi gyaran da ya dace,” in ji shi.

Jama’a sun yi mamakin sanarwar farfaɗo da masana’antar a ƙarshen shekarar da ta gabata. Masana’antar, mai samar da ganga 60,000 a rana, tana aiki da kashi 70 cikin 100 na ƙarfinta. Farfadowarta ta kasance wani muhimmin mataki na rage dogaro da Nijeriya ke yi kan shigo da man fetur. Gwamnatin Nijeriya ta amince da gyaran masana’antar kan kuɗi dalar biliyan 1.5 a shekarar 2021.

Masana’antar tana samar da lita miliyan 1.4 na man fetur, lita miliyan 1.5 na dizal, lita miliyan 2.1 na mai mai nauyi, lita 900,000 na Kananzir, da kuma iskar gas (LPG). Farfadowarta ta kasance muhimmin mataki na samun ‘yancin cin gashin kanta a fannin makamashi da kuma ci gaban tattalin arziƙi.

NLC: “Masana’antar Ba ta Aiki”

Chris Onyeka, mataimakin sakataren NLC, ya ce dama cab NNPCL ba ta aiki don haka ba zai yiwu a ce an rufe abin da baya aiki ba. Ya ce, “Gwamnati tana ɗaukar jama’ar Nijeriya a matsayin basu san me suke ba; ba su da gaskiya, kuma muna ganin suna ɓatawa kansu suna ne da gangan. Ta yaya za su ce masana’antar Fatakwal tana aiki, tare da ta Dangote, amma har yanzu muna shigo da man fetur?

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

gaza
Manyan Labarai

Majalisar Dattawa Ta Maido Da Ranar Tantance Sabbin Shugabannin Sojoji Zuwa Laraba

October 28, 2025
An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato
Manyan Labarai

An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

October 28, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno
Manyan Labarai

Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno

October 28, 2025
Next Post
Rikici Ya Ɓarke Tsakanin ‘Yansanda Da Matasa A Rano, Mutum 1 Ya Mutu, An Harbi Wasu

Rikici Ya Ɓarke Tsakanin 'Yansanda Da Matasa A Rano, Mutum 1 Ya Mutu, An Harbi Wasu

LABARAI MASU NASABA

gaza

Majalisar Dattawa Ta Maido Da Ranar Tantance Sabbin Shugabannin Sojoji Zuwa Laraba

October 28, 2025
Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani

Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani

October 28, 2025
Ina Fatan Buga Kofin Duniya Na 2026 — Messi

Ina Fatan Buga Kofin Duniya Na 2026 — Messi

October 28, 2025
Tsohon Kwamishina Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Sayar Da Filin Makaranta Kan Miliyan 100

Tsohon Kwamishina Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Sayar Da Filin Makaranta Kan Miliyan 100

October 28, 2025
An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

October 28, 2025
’Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Ƙone Gidan Shugaban Jam’iyyar PDP A Bauchi

’Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Ƙone Gidan Shugaban Jam’iyyar PDP A Bauchi

October 28, 2025
Mutum 18 Sun Mutu, 40 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Kebbi 

An Kashe Mutum 10 A Harin Ramuwar Gayya A Jihar Kebbi

October 28, 2025
Ganduje Na Kara Shan Matsin Lamba A Kan Ya Sauka

Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar  Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu

October 28, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno

October 28, 2025
Fatakwal

APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba

October 27, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.