Kyaftin din Liverpool Virgil van Dijk ya amince da cewa har yanzu akwai sauran aiki kafin a fara kakar wasa ta bana bayan da kungiyar ta sha kashi a hannun Bayern Munich da ci 4-3
Reds ta ci kwallaye biyu a wasan share fage a Singapore, inda Cody Gakpo da Van Dijk suka jefa kwallo.
Serge Gnabry da Leroy Sane ne suka daidaita al’amura a Bayern, sai dai Luis Diaz ya maido da Wasan danye bayan ya jefawa Liverpool kwallo ta uku
Sai dai Josip Stanisic ya rama kwallon kuma Frans Kratzig ya zurawa Bayern kwallo ta hudu a minti na 91
Van Dijk mai shekaru 32 ya gaya wa LFCTV cewa akwai abubuwa masu kyau da yawa da kuma abubuwan da ya kamata mu inganta
Akwai babban aiki har yanzu kuma abin da muke kokarin mu yi ke nan
Liverpool ta zura kwallaye 15 a wasanni hudu na tunkarar kakar wasa ta bana, amma an zura mata kwallaye 10 yayin da take ci gaba da neman dan wasan tsakiya
Ya kara da cewa Muna da ingancin da za mu hukunta su idan sun yi kuskure kuma abin da muka yi ke nan
Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya tabbatar bayan wasan da cewa Liverpool ba ta wata matsala duk da cewa dan wasan tsakiya Alexis Mac Allister ya samu rauni a gwuiwarsa