Babban hafsan hafsoshin tsaron Nijeriya (CDS), Janar Christopher Musa, ya nuna damuwarsa game yadda masu aiki a kasa da kasa ke daukar nauyin kungiyar Boko Haram da sauran kungiyoyin ta’addanci da ke tada zaune tsaye a kasar fiye da shekaru 15.
Janar Musa ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Aljazeera a kwanan nan, wanda wakilinmu ya rahoto.
- Wakilin Musamman Na Xi Ya Halarci Bikin Rantsar Da Shugaban Ghana
- An Kashe ’Yan Ta’adda 34 Da Sojoji 6 A Harin Borno – Shalkwatar Tsaro
CDS ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya (MDD) da ta binciki hanyoyin samar da kudade da makamai da ‘yan ta’addan ke amfani da su, inda ya kara da cewa, mayakan da suka mika wuya sun mallaki wasu makudan kudade na kasashen waje.
“Mun tattauna da al’ummomi da dama a fadin duniya kan wannan ta’addancin don gano masu daukar nauyin ta’addancin. A yayin da muke wannan maganar, fiye da ‘yan Boko Haram 120,000 ne suka mika wuya, kuma akasarinsu sun mallaki makudan kudi irin na kasashen waje. Ta yaya suka same su? Wake daukar nauyinsu? Ta yaya suke samun horo? Ta yaya suke samun makamai da sauran kayayyakin ta’addanci?” Tambayoyin Janar Musa
Ya jaddada cewa, MDD ce kadai ke da iko da hurumin ganowa da bin diddigin masu daukar nauyi da tallafawa ayyukan Boko Haram. “Akwai buƙatar Majalisar Dinkin Duniya ta shigo cikin wannan lamarin saboda muna bukatar gano ta inda kudaden ke shigowa,” in ji shi.