Kungiyar masu hakar ma’adanai da sarrafashi ta kasa ta bayyana cewa akwai bukatar gwamnatin tarayya ta kara bayar da himma wajem inganta harkokin hakar ma’adanai domin bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasa baki daya.
Haka zalika, kungiyar ta ce lokaci yayi da gwamnatocin kasar nan za su himmatu wajen samar da yanayi mai kyau domin inganta hakar ma’adanai wajen farfado da komadar tattalin arzikin kasar nan.
- Sin Ta Samar Da Kudade Domin Tabbatar Da Hidimar Dumama Muhalli Yayin Hunturu Ga Mutanen Da Ibtila’i Ya Shafa
- Sin Ta Kafa Tasoshin Sigina Ta 5G Fiye Da Miliyan 4.1
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin shugaban kungiyar na kasa, Injiniya Umar Hassan a wani wani taron shekara-shekara na kumgiyar wanda ya gudana a Jihar Kaduna.
Ya ce hakar ma’adanai na taimakawa wajen bunkasa ci gaban tattalin arziki da kuma magance matsalar rashin da ya addabi matasan kasar nan, yana mai cewa muddin aka inganta harkar ma’adanai babu shakka Nijeriya za ta zama kan gaba wajen bunkasar tattalin arziki a fadin duniya.
Shugaban ya ce taron na bana ya mayar da hankaline wajen yadda za a inganta hakara hakar ma’adanai. Ya kara da cewa kungiyarsu ta himmatu wajen tabbatar da cewa an kawo masu zuba hannun jari wajen hakar ma’adanin.
Da yake bayani dangane matsalar masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, ya ce kungiyarsu ta himmatu wajen tabbatar da cewa duk wadanda za su fara hakar ma’adanai sun bi ka’ida. Ya yi kira ga gwamnatin tarayya da na jihohi da su tabbatar da cewa sun samar da yanayi mai kyau wajen bai wa masu hakar ma’adanai damar da ya kamata domin bunkasa ci gaban tattalin arzikin kasar nan baki daya.
A nasa wajabin, shugaban kungiyar na Jihar Kaduna, Injiniya Mohammed Nura Sani Hussain, ya ce gudanar da taruka irin wanna zai taimaka kan fadakar da gwamnati wajen alfanu da ribar da cikin hakar ma’adanai. Ya ce lokaci ya yi da gwamanati za ta tabbatar da cewa ta samar da yanayi mai kyau domin inganta harkar ma’adanai a fadin kasar nan.