Sabuwar Mai Bada Shawara Kan Harkokin Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, Maryam Bukar-Hassan (Alhan-Islam) ta bayyana cewa samun dauwamammen zaman lafiya a duniya shi ne burinsu.
Da yake gabatar jawabi a yayin maraba da ita a ofishinsa dake Abuja, Babban Jami’in Kula da Ayyukan Jin Kai na Majalisar Dinkin Duniya Mohammed Malick Fall, ya jaddada muhimmancin samar da zaman lafiya, yana mai cewa zaman lafiya wani abu ne da ake bukata don jin dadin rayuwar dan’Adam, kuma idan ba a same shi ba, ci gaban dimokuradiyya da kuma ’yancin dan’Adam ba zai samu ba.
- UBEC Ta Kaddamar Da Makarantun Zamani 21 A Sassan Nijeriya
- Tetfund Ta Samar Da Naira Biliyan 100 Don Inganta Ilimin Likitanci – Masari
Ya bayyana damuwarsa kan yadda aka sake samun bullar tashe-tashen hankula a Nijeriya da ma duniya baki daya, yana mai cewa hakan koma baya ne ga ci gaban da aka samu tun kafuwar MDD shekara 80 da suka gabata. Har ila yau, Mohammed Fall ya yaba da nadin Maryam Bukar-Hassan a wannan matsayin, yana mai cewa hakan ya zo a daidai lokacin da ya dace kuma mai mahimmanci, yana mai bayyana irin karfin gwiwar da yake da shi a kanta na sauke nauyin da aka dora mata, musaman wajen isa ga al’umma da matasa ta hanyoyin diflomasiyya.
Yana mai cewa, “Ku ne muryar matasa, muryar jagorancin mata.” Ya kuma jaddada irin rawar da taka wajen tsara makomar neman zaman lafiya.
Ya kuma bayyana cewa, nauyin da ke kanta ya yi fice a Nijeriya har zuwa ayyukan da duniya ke yi. Duk da irin rawar da take takawa a duniya, Fall ya ba ta tabbacin goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya.
Ita ma da take nata jawabin Maryam Bukar Hassan ta ce, akwai bukatar a samar da wani shiri na kawo sauyi wajen samar da zaman lafiya mai dorewa.
Hakazalika Maryam ta jaddada cewa, idan har ba zaman lafiya babu yadda za a iya cimma muradun ci gaba mai dorewa (SDGs) kuma zai kasance mara amfani.
“Ba maganar talauci idan zaman lafiya da adalci sun tabbata.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp