A yau mun kawo muku hira da wata ‘yar kasuwa mai suna Khadija Ahmad wadda ta shahara wajen kasuwancin zamani na KIRITO. Harkar Kirifto wani bangaren na kasuwanci da al’umma da dama basu sani ba wasu kuma na dar-dari dashi. A wannan hirar Malama Khadija Ahmad ta yi mana bayani filla-filla a kan yadda mutum zai samu nasara a harkar kasuwanci na Kirifton Ga dai yadda hirar ta kasance.
Da farko za mu so sanin cikakken sunanki da tarihinki?
Assalamu Alaikum Warahmatullahi Wabarakatuhu. Sunana Khadija Ahmad, amma an fi kirana da Ummu Nafisat, kuma ni Basakkwaciya ce haifaffiyar Garin Kaduna, amma yanzu ina zama ne a gidan gwamnatin Jihar Lafia a Karamar Hukumar Maraba Karu.
- Emefiele Ya Yi Amfani Da Wakili Wajen Karbar kwangila Daga CBN – Shaida
- Hukumar Haraji Ta Nemi A Samar Da Dokar Sa Ido A Kan ‘Yan Kirifto
Shin Khadija matar aure ce?
Kwarai kuwa ni matar aure ce har da ‘ya’yana maza da mata. Kuma Sunan mijina Usman Shehu Shagari
Kina sana’a ko aikin gwamnati?
Eh, ina kasuwanci
Wane irin kasuwanci kike yi?
Harkar Kirifto nake yi
Shi wannan kasuwancin yaya yake ko kuma na ce ya ya ake yin sa?
Ni kasuwanci na shi ne kirifto wato (Crypto Currency) a turance wato meta force.
Toh ita harka crypto currency ya kunshi abubuwa da yawa amma yanzu jama’armu daga sun ji an ce crypto currency sai su yi tunanin cewa mining, amma ya kunshi abubuwa da yawa don meta force decentralized aiki ne wanda yana kan block chain shi ya sa ya shiga cikin crypto. In aka ce abu yana block chain to an riga an tsara shi akai, wanda ya kirkira ma bai isa ya canja shi akan tsarin da ya sa ka shi akai ba. Shi meta force ya kunshi abubuwa da yawa ta ba garin crypto kuma yana da nashi tsarin na kashin kansa.
Me ya ja hankalinki har kika shiga wannan kasuwancin?
Abin da da ya jawo hankalina har na shiga cikin wannan kasuwanci kawai na gani a cikin wani group ne ana tallansa, ni kuma a ranar da na fahimci abin kuma na ga yadda mata da maza suke sumun alkhari a cikinsa da kuma yadda malamai suke bayani akan sa musamman na Shiek Albani Zariya. Sai na ji ina son abin sai na yi istihara daga nan sai na yi registration lebel 1 kasancewar yana da tsari na iyakar kusan shekarata biyu kenan, a lokacin ana yin lebel akan Naira 4,700.
Malama Khadija kince ana samun alkhairi akan shi wannan kasuwanci na Kirifto, ta yaya ake samun alkhairin?
Shi bangaran da ake samun kudi a mete force bangaran kawo mutane, idan kana kawo mutane kamfani za su rinka biyan ka da Daloli saboda suna son yawan mutane wato (Community) a turance, kuma a tsarinmu na Hausawa kowa ya san yawan mutane shi ne kasuwa ba wai yawan rumfuna ba kamfani suna biyan mutane idan yana da yawan kawo mutane, sannan akwai spillober da ober pilot na team da yake yawo a tsakanin mutane wanda idan ka gayyato mutum ya yi rijista na daya da na biyu ba za ka samu ba zai fi a team ya fadawa mai rabo ko a matsayin Dala ko kuma a matsayin kafa na uku da hudu da biyar duk za ka samu dalolinsu, kamar lebel a ka’ida za ka samu Dala 15 lebel 2 30 Dala, 3 40 Dala haka dai yana sau biyun na baya har zuwa lebel din karshe. Har yanzu muna kaddamarwa kyauta ne ( free Lunching) a turanci idan aka zo aka yi lancin din sa sai ya fi haka.
Malama Khadija a yanzu kina lebel 1 din ko kuma da an samu ci gaba ko akasin haka?
To Alhamdulillah gaskiya babu abin da zan ce da Allah sai hamdala saboda na samu ci gaba sosai har na kai lebel 12 wanda shi ne lebel na karshe bawai da waya daya ba da wayoyi biyu, kuma da wannan lebel 1 din ina samun alkhairi har na kai haka wanda a yanzu lebel 12 idan aka lissafa ya kai 16,000 000 kenan to kin ga ai sai dai na yi ta yi wa ubangiji godiya ban da kudin da na ci ban san iya adadin milyan din ba.
Mene ne matakin karatunki
Toh na yi karatu na a Garin Kaduna Kwanar Cancanji na yi daga firamare har sakandire daga nan na tsaya.
Lokacin kina makaranta mene ne burinki?
To daman ni burina shi ne kasuwanci, bayan na gama makaranta sai na ci gaba da kasuwancina dama can ina da burin zama fitatacciyar ‘yar kasuwa.
Karatu fa?
A’a ba ni da burin ci gaba da karatu wanda na yi ma Allah ya sa masa albarka.
Ko za ki iya fadawa masu karatu wadanne irin nasarori kika samu a cikin wannan kasuwanci?
Toh Alhamdulillah alhamdulillah nasarori ai ba su musaltuwa akwai nasarori iri- iri zumunci tsakaninmu da girmama juna, sannan abu mafi dadi a cikin tafiyar meta force shi ne duk wanda ka janyo shi cikin wannan tafiyar zai kasance kullum yana cikin yi maka addu a saboda zai samu alkharai da bai taba tunanin cewa zai samu a rayuwarsa ba kuma babbar nasarar mu shi ne force coin dinmu, wanda mun saye shi ne a 0.5 dollar ya do yana tashi kadan-kadan ya do 2.77dollars yadda a lokacin inda na kasa saya akan 0.5 na dollar 50 za’a baka guda 200, ya do yana tashi ana rage yawan shi.
Yanzu de force coins tsakanin watan daya da ya wuce zuwa wannan wata har ya doka 22dollars kowanne coins sai ya do mutane suka fara saya sai mai kamfanin wato Mr Lado da ya ga sai ya saukar da shi saboda ba ya so a wulakantar mai da coins sai ya saukar da farashin coins din zuwa 9.5 yana hawa kuma zuwa Dala 11, to shi ne abin da duk wani dan meta force yake alfahari da shi.
Wanne abu ne yafi faranta miki rai game da wannan kasuwancin?
To abin da yake faranta min rai sosai shi ne duk wanda ka janyo yana alfahari da kai kuma kullum idan ya ki saukar da Dala a wallet dinsa sai ya yi maka addu’a ya kira ka yana farin ciki da godiya, sai kuma force coins wanda muka saya kudin da bai kai #100 ba amma yanzu yana buga kusan #16,000 abu sati daya da ya wuce sai da ya buga #30,000 to ina matukar farin ciki in na tuna da haka kuma mutane na farin ciki.
Dame kike so mutane su rika tunawa dake?
Ina so mutane su rinka tunawa da ni akan ta sanadiyar Ummi Nafisat suka shigo mete force kuma suke samun alkhairi wasu suna taimakawa iyaye da ‘yan uwa da kuma jama’ar Musulmi.
Ga fama da jama’a ga gida da yara, maigida yana samun kulawa dari bisa dari kuwa?
Ina zuwa Islamiya kuma Alhamdulillah mun yi saukar Alkur’ani kuma muna hadda zan tafi Islamiya in dawo, sannan na yi aikace-aikacen gida na ina kula da yara da maigida sosai yana samun kulawa ba shi da wata matsala kuma na ci gaba da kasuwanci na a saukake ta wayata a gidana ina kwance a dakina.
Ko za ki bayyana wa masu karatu wace irin addu’a ce idan aka miki kike jin dadin ta?
Idan aka ce Ummu Nafisat Allah ya saka muku da alkhairinsa ya jikan iyayenki, in suna raye Allah ya kara musu lafiya ya kare ki daga sharrin makiyanki ya shirya miki zuri’anki ya daukaka ki ina matukar jin dadin wannan adu’o’in.
To a karshe wacce irin shawara za ki ba wa mutane a kan wannan sana’a taki?
Ina ba wa ‘yan uwana mata har da mazan ma da su zo su rike wannan kasuwancin na mete force wanda alkhairi ne na har aba da musamman ma mutanenmu ‘yan Arewa saboda ‘yan Kudu sun yi mana nisa sosai a kansa sun fahimce shi da kyau, mu kuma ‘yan Arewa duk wani abin arziki sai ki ga muna sakaci da shi har sun wuce mu