Akwai yiwuwar majalisar kasa ta yi wa kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 kwaskwarima domin samar da kofar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) za ta iya gudar da zaben kananan hukumomi kai tsaye, ba hukumar zabe na jihohi ba.
Wannan na zuwa ne bayan hukuncin kotun koli wacce ta bai wa kananan hukumomi ‘yancin gashin kansu, sakamakon karar da gwamnatin tarayya ta shigar a gabanta.
Da yake mayar da martini kan lamarin lokacin taron ‘yan jarida a Abuja, dan majalisan dattawa mai makiltar Kogi ta yamma, Sunday Karimi ya bayyana cewa majalisa za ta tabbatar da cewa gwamnonin jihohi sun yi bara’a ga hukuncin kotun koli tare da gyara kundin tsarin mulki domin shigar da sabbin batutuwa.
- Za Mu Sa Kafar Wando Daya Da Masu Digirin Bogi A Nijeriya – Minista
- Tsadar Rayuwa: ‘Yan Majalisa Sun Rage Albashinsu Da Kashi 50 Cikin 100
Dan jamalisar ya ce, “Cikin abubuwan da za a gyara akwai mayar da gudanar da zabe karkashin hukumar zabe ta kasa daga wurin hukumomin zabe na jihohi.”
Sanatan ya kara da cewa har yanzu tsugue ba ta kare ba, domin wasu gwamnonin za su kalubalanci lamarin.
“Shugaban kasa Bola Tinubu ya sakar wa bangaren shari’a mara wajen gudanar da wannan shari’a ba tare da la’akari da cewa yana zangon farko ne na shugabancin kasa wanda zai so ya kara yin zago na biyu a 2027,” in ji Karimi.
Kazalika, dan majalisan dattawa mai wakiltar Delta ta tsakiya, Okakuro Ede Dafinone ya ce bisa samun wannan ci gaban, za a yi wa kundin tsarin mulkin Nijeriya kwaskwarima, domin bai wa INEC daman gudanar da zaben kananan hukumomi kai tsaye a hukumance.
Ya ce “Abun takaici ne a ce mutane ba sa amfana da tsarin dimokuradiyyarmu sakamakon yadda gwamnoni suka ki sakar wa kananan hukumomi mara wajen bari a zabi kansiloli da shugaban kananan hukumomi.
“Gwamnoninmu ne suke zaben shugabannin kananan hukumomi da kansu a jihohinsu. Idan a ce INEC za ta gudanar da zabe kamar yadda gwamnoni suke zaben kananan hukumomin, da yawa daga cikinsu ba za su zama gwamnoni ba a yau.
“Ina tunanin wanna shi ne karo na farko a tarihin kasar nan da kuma dimokuradiyyarmu, za mu yi watsi da bambancin siyasa wajen hada kai mu yi aiki tare domin gyara wani bangare na tsarin mulkinmu wajen ceto kananan hukumomi daga hannun gwamnoninmu.
“Ina yaba wa kokarin Shugaban kasa Bola Tinubu bisa wannan tunani na tabbatar da ‘yancin kananan hukumomin kasar nan.
“Za mu yi aiki da tsarin dimokuradiyya a matakin kananan hukumomi wajen tabbatar da INEC ta gudanar da zaben kananan hukumomi a fadin kasar nan, domin bai wa mutanenmu damar shiga harkokin gwamnatin dimokuradiyya.”
Sanata Dafinone siffanta zaben kananan hukumomin da ya gudana a Jihar Delta a matsayin abun kunya ga tsarin dimokuradiyya.