Ko shakka babu kamar yadda alakar sauran kasashen duniya masu karfin tattalin arziki take gudana, Sin da kasashe membobin kungiyar tarayyar Turai ta EU suna da nasu sabani. Amma sabani ba daidai yake da fito-na-fito ba. Hasali na daidai ta hanyar shawarwari ne kadai ake iya warware bambance-bambance, har a kai ga cimma moriyar juna cikin lumana.
Idan mun duba tarihi, za mu ga cewa a bana alakar Sin da EU take cika shekaru 50 da kafuwa, wanda hakan babbar nasara ce da sassan biyu suka cimma, bayan shafe gomman shekaru suna shawarwari, da hadin gwiwa da cimma moriya tare. Tabbas wannan muhimmin lokaci ne na waiwayen baya, da jinjinawa muhimmin kawance na tsawon lokaci dake ci gaba da wanzuwa tsakanin sassan biyu.
- Anacláudia Rossbach: Ya Kamata Kasashen Afirka Su Koyi Darasi Daga Sin Na Kawar Da Talauci Da Kyautata Kauyuka Zuwa Birane
- Masu Zuba Jari Na Kasa Da Kasa Sun Gamsu Zuba Jari A Sin Dama Ce Ta Cimma Nasarar More Riba A Nan Gaba
Masharhanta na cewa, duk da sabani a wasu sassa dake bullowa lokaci bayan lokaci tsakanin Sin da EU, a daya bangaren sassan biyu sun more muradun bai daya, musamman gajiyarsu ta fuskar cinikayya, da yaki da sauyin yanayi da jagorancin duniya.
A fannin raya cinikayya kuwa, darajar cinikayyar Sin da EU ta karu daga dalar Amurka biliyan 2.4 a shekarar 1975 zuwa kusan dala biliyan 785 a shekarar 2024, ta yadda alakar tattalin arzikinsu ta zamo daya daga mafi karfi, dake ingiza bunkasar tattalin arzikin duniya baki daya. Karkashin hakan, an ga yadda zirga-zirgar jiragen kasa na dakon kaya ke kara habaka tsakanin sassan biyu. A daya bangaren kuma zuba jari domin raya masana’antu tsakanin sassan biyu shi ma ya yi matukar karuwa. An kuma fadada hada-hada a fannonin yawon bude ido, da ilimi, da musaya tsakanin al’ummun Sin da Turai.
A wannan gaba da alakar Sin da Turai ta kai wani muhimmin lokaci a tarihi, kuma sassan biyu ke alfahari da nasarorin da suka cimma, da gajiyar da suke samu a hada-hadar cinikayya, da raya tattalin arziki da sauran muhimman fannoni, abun da ya dace shi ne sassan biyu su kara kwazon aiwatar da matakan yaukaka amincewa da juna, da gina gadar fahimtar juna. Ko shakka babu Sin da EU za su iya cimma wannan nasara, idan sun rungumi ainihin ruhin alakarsu, wato martaba juna, da cimma moriya tare, da kuma raba ribar nasarorin da suke samu. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp