Shugaban kasar Serbia, Aleksandar Vucic, ya ce kasarsa na goyon bayan Shawarar Kula Da Harkokin Duniya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar.
Shugaba Vucic ya bayyana haka ne yayin da yake hira da wakilin CMG a birnin Beijing na kasar Sin a kwanan baya, inda ya ce tsarawa da gabatar da wannan shawara mai ma’ana, ya zama wani abun da ya wajaba, saboda da farko, a zamanin da ake ciki, ana bukatar samar da karin ikon wakilci ga kasahe masu tasowa a fannin kula da al’amuran kasa da kasa. Kana na biyu, yanzu sannu a hankali ana lalata sakamako da nasarorin da dan Adam ya samu ta fuskar dokoki da ka’idoji na kasa da kasa, yanayin dake bukatar a sauya shi. Sa’an nan dalili na 3 shi ne, matsalar da ake fuskanta ta rashin ingancin aiki a fannin tabbatar da dorewar ci gaban duniya, da tinkarar sauyawar yanayi, da cika alkawuran da gwamnatoci daban daban suka yi wa dan Adam.
A cewar shugaban na kasar Serbia, burin da shugaban kasar Sin Xi Jinping yake neman cimmawa, ta hanyar gabatar da wannan shawarar, shi ne tabbatar da daidaito tsakanin kasashe da al’ummu daban daban, gami da ba jama’a damar cin gajiyar duk wani mataki da ake dauka. Saboda haka, Mista Vucic ya ce ya kamata kowane mutum, da shugaban duk wata kasa, su goyi bayan shawarar ta kula da harkokin duniya, saboda tana da kyakkyawar manufa, kuma kasar ba ta da niyyar lalata tsarin kasa da kasa da ake kai yanzu. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp