A makon da ta gabata ne, Majalisar Sarakunan Yarabawan Unguwar Awori Igbasa da ke yankin Agbara karkashin Mai Martaba Sarkin Yarabawa, Oba Mohomod Saeed Idioke na Jihar Ogun ta nuna amincewarta tare da ba da izinin nada Alhaji Amadu Umar, a matsayin Sarkin Hausawan garin Agbara da kewayenta.
Taron nadin sarautar ya samu halartar wadansu daga cikin sarakunan Yarabawa da na Hausawan mazauna Jihar Ogun da Legas da sauran al’umma baki daya. Taron ya gudana ne a harabar fadar Mai Martaba Sarkin Yarabawan yankin na Idioke da ke garin Agbara.
- Jami’ar Kiwon Lafiya Ta Legas Za Ta Kara Samar Da Kwararru – Kwamishina
- Dalilin Da Ya Sa Legas, Abuja, Kaduna Suka Samu Masu Zuba Hannun Jari A Zango Na Uku
Alhaji Amadu ya kasance dan asalin Jihar Jigawa mazaunin Jihar Ogun, inda Sarkin Yarabawan ya ummurci sakataren fadarsa tare da ba shi izinin karanto kyawawan halayen Sarkin Hausawan da kuma bayyana dalilan da suka sa Majalisar Sarakunan Yarabawan ta ba shi wannan sarauta.
Sakataren fadar sarkin Yarabawa ya ci gaba da bayyana cewa Majalisar Sarakunan Yarabawan ta amince da nadin Alhaji Amadu a matsayin Sarkin Hausawan garin Agbara bisa kyawawan halayensa da kuma kokarinsa na hada kan Hausawa da sauran kabilun Yarabawa mazauna yankin, domin su ci gaba da samun zaman lafiya a tsakaninsu baki daya.
Ya ce sun kwashe shekaru da dama suna cudanya da shi ta fuskar zaman lafiya da sauran al’amuran rayuwa na yau da kullum. Bugu da kari, sakataren sarkin Yarawan ya ci gaba da cewa tun daga lokacin da suka san juna da Alhaji Amadu zuwa yanzu ba a taba samun shi yana rigima da wani ba.
Sabon Sarkin Hausawan na garin Agbara a Jihar Ogun, Alhaji Amadu ya yi jawabin godiya ga Majalisar Sarakunan Yarabawan unguwar Awori Igbasa da ke yankin Agbara dangane da cancantar da suka ga ya yi suka ba shi wannan sarauta.