Alhazan Nijeriya na ci gaba da shiga garin Madina a matakin farko na gabatar da aikin hajjin bana, inda da damar su da wakilinmu ya tattauna da su, sun bayyana gamsuwarsu da irin ƙoƙarin da jami’an Hukumar Alhazai ta Nijeriya NAHCON ke yi wajen tabbatar da jin dadinsu a yayin da suke garin Madina.
Hajiya Rabi’atu Musa daga jihar Kogi ta ce, ‘Tun daga Nijeriya har muka shigo Madina jami’an NAHCON sun tabbatar da komai na tafiya daidai’, ta ce, masauki da abincin da aka ba su abin a yaba ne.
- Hajjin 2024: Ranar 10 Ga Watan Yuni Za A Kammala Jigilar Maniyyata – NAHCON
- Aikin Hajji 2024: NAHCON Ta Kwashe Maniyyata 7,582 Don Sauke Farali
Daga karshe ta nemi NAHCON ta samar da jami’ai masu Larabci da kuma yarukan mu na gida, domin ana yawan samun matsala wajen tattaunawa tsakankin Alhaji da wasu jami’an hukumar da kuma Larabawa a wasu lokuta.
Shi kuwa Alhaji Yunusa Abdullahi daga Babban Birnin Tarayya Abuja ya nemi Alhazai su ba jami’an NAHCON goyon baya domin samu cikakkiyar nasara a aikin Hajjin bana.