Ali Nuhu Muhammad ko kuma Sarki Ali Nuhu kamar yadda ake kiransa a masana’antar Kannywood inda ya shafe shekaru fiye da 25 yana nuna bajintarsa ta wasan kwaikwayo, ya zamo wani ginshiki a masana’antar Kannywood tsawon wadannan shekaru.
Ali Nuhu wanda ya fara harkar fim a shekarunsa na kuruciya bayan da ya kammala aikinsa na bautar kasa,ya zama daya daga cikin jaruman da tauraruwarsa ta dade tana haskawa a masana’antar, daga jarumi zuwa mai daukar nauyi kuma zuwa mai bayar da umarni a masana’antar wanda yanzu haka shi ne shugaban hukumar Fina Finai ta Nijeriya mukamin da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bashi duba da kwarewa da gogewarsa a harkar.
- Wuraren Kiwo: Fulani Sun Yi Murna Da Matakin Shugaban Kasa – Ngelzarma
- Al’adar Tashe A Kasar Hausa
Ali Nuhu Mohammed an haife shi a ranar 15 ga watan Maris a shekarar 1974,ya auri Maimuna Garba a shekarar 2003 inda suka haifi ‘ya’ya 2 Ahmed da Fatima.
Ali Nuhu dan wasan kwaikwayo ne da ya yi shura a ciki da wajen Nijeriya wanda yanzu haka shi ne manajan darakta na hukumar Fina-Finan Nijeriya wanda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada shi ranar Juma’a 12 ga Janairu 2024.
Kafin nadin nasa, fitaccen dan wasan kwaikwayo ne kuma darakta inda yake fitowa a fina-finan Hausa da na turanci, sannan kuma ana kiransa da Sarkin Kannywood ko kuma Sarki Ali.
Ali Nuhu ya fito a fina-finan Nollywood da na Kannywood sama da 500, kuma ya samu lambobin yabo da dama, ana kallon Ali Nuhu a matsayin daya daga cikin fitattun jaruman fina-finan Hausa a tarihi, kuma an bayyana shi a matsayin wanda ya fi samun nasara a fim din Hausa.
Ali ya fara fitowa a fim din Abin Sirri ne a shekarar 1999,ya kuma shahara sanadiyar rawar da ya taka a fim din Sangaya, wanda ya zama daya daga cikin fina-finan Hausa da suka fi samun kudi a lokacin, ya haskaka a fina-finai da dama, da suka hada da Sai Watarana,Ali,Alaka da sauransu shi ya samu kyautar Gwarzon Jarumi a wajen bayar da lambar yabo ta African Mobie Academy Awards (2007).
A shekarar 2019 Ali Nuhu ya yi bikin cika shekaru 20 a harkar nishadantarwa inda ya fito a fina-finai kusan dari biyar, yana daya daga cikin fitattun jaruman fina-finan Hausa, ya kan fito a jerin fitattun mutane,masu tasiri a Nijeriya.
Ya kasance yana fitowa a kai a kai cikin manyan mutane goma daga cikin 100 mafiya tasiri a Nijeriya ya kuma kasance jakadan kamfen na gwamnati da na sa-kai da suka hada da Globacom,YALE da sauran su.