Alkaluman hukumar kididdiga ta kasar Sin NBS, sun nuna karuwar adadin sayar da kayayyaki na kamfanonin kasar ko PMI, da maki 49.2 a watan nan na Nuwamba, wanda hakan ke shaida karuwar kaso 0.2 bisa dari kan na watan da ya gabaci hakan.
Alkaluman da NBS ta fitar a Lahadin nan, suna kan mizanin sama da kaso 50 mai tabbatar da karuwar hada-hada, yayin da kasa da 50 ke nuna koma baya. Sun kuma tabbatar da ci gaban fannonin samar da hajoji da na bukatarsu.
Fannin samar da hajoji ya kai maki 50.0, karuwar da ta kai ta kaso 0.3 bisa dari sama da na watan Oktoba, adadin da ya kai muhimmiyar gabar ci gaba. Bangaren sabbin bukatun sayayya kuwa ya kai maki 49.2, adadin da ya karu da kaso 0.4 bisa dari.
Game da masana’antu daban daban kuwa, sashen samar da hajoji da alkaluman sabbin odar su, a fannoni irinsu na sarrafa albarkatun noma, da na sarrafa dangogin karafa ya samu tagomashi, wanda hakan ya shaida bunkasar sassan sarrafawa da na bukatar masu sayayya.
A bangaren manyan fasahohi kuwa, sashen ya samu ci gaba, inda alkaluman PMI ya kai maki 50.1, sama da mizanin muhimmiyar gabar ci gaba cikin watanni 10 a jere.
NBS ta tabbatar cewa, alkaluman PMI na sashen masana’antun da ba na sarrafa hajoji ba, sun kai maki 49.5 a watan nan, raguwar da ta kai ta kaso 0.6 bisa dari kan na watan da ya gabaci hakan. (Saminu Alhassan)














