A yau Laraba ne kungiyar kanana da matsakaitan masana’antu ta kasar Sin, ta sanar da cewa, alkaluman ci gaban wannan rukuni na masana’antu ko SMEDI a takaice sun kai 88.9 a watan Janairun bana, wanda hakan ya nuna karuwar alkaluman sama da na watan Disamban bara, duk da cewa a farkon shekarar bara alkaluman sun rika raguwa.
Yanzu haka an shawo kan yaduwar annobar cutar COVID-19 a kasar Sin, don haka alkaluman ci gaban sana’o’i 8 na kasar, sun karu a watan Janairun bana, musamman ma a bangarorin sufuri, da zirga-zirga, da hidimomin otel, da dakunan cin abinci, wadanda ke samun cunkoson jama’a.
A halin yanzu, matakan sarrafa yaduwar annobar da gwamnatin kasar Sin ta dauka, domin ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’umma, sun samu sakamako a bayyane, kuma tattalin arzikin kasar yana farfadowa a sannu sannu.
A sa’i daya kuma, gwamnatin kasar Sin ta fitar da wasu manufofin gata, domin tallafawa kanana da matsakaitan masana’antu, kuma ko shakka batu, kokarin da gwamnatin kasar take yi zai ingiza ci gaba mai inganci, a fannin kanana da matsakaitan masana’antu. (Mai fassarawa: Jamila)