Yawan GDPn kasar Sin cikin kason yawan GDPn kasar Amurka, ya dade yana zama muhimmin batun da jama’a ke tattaunawa, musamman tun bayan da ita Sin din ta zama kasa mafi karfin tattalin arziki ta biyu a duniya. A shekara ta 2023, wannan adadi ya ragu. To, da aka gano wannan sauyi, tare kuma da yin la’akari da yadda Amurka take yi wa kasar Sin kangiya da danniya, mutane da yawa na ganin cewa, shin tattalin arzikin kasar Sin zai tawaya?
Amma wannan gaskiya ce?
Bari mu duba wannan adadi, wato kidayar yawan GDP na wata kasa, wanda ya shafi fannoni daban-daban, ciki har da farashin kayan masarufi da darajar kudi da sauransu. A shekaru ukun da suka gabata, Amurka ta gabatar da wasu tsauraran manufofin hada-hadar kudi, al’amarin da ya janyo mummunar matsalar hauhawar farashin kaya a kasar, kuma hakan ya habaka yawan GDPn kasar.
Alal misali, a shekara ta 2022, yawan CPI da yawan PPI na kasar Amurka, sun karu da kaso 8 bisa dari, da kaso 16.5 bisa dari, yayin da yawan CPI da yawan PPI na kasar Sin, suka karu da kaso 2 bisa dari, da kaso 4.1 bisa dari. Ke nan ana iya fahimtar irin “gibi” da aka samu, yayin da aka kidaya su.
Ban da farashin kaya, yayin da ake kwatanta yawan GDPn kasashe daban-daban, a kan kuma yi la’akari da darajar kudin musanya. Wato idan ana son kwatanta yawan GDPn Sin da na Amurka, ya kamata a sauya yawan GDPn kasar Sin da aka kidaya da kudin kasar wato Yuan, zuwa dalar Amurka. Tun daga shekaru biyu da suka wuce, Amurka ta fara sabon zagayen kara kudin ruwa, inda tun daga watan Maris din shekara ta 2022 zuwa watan Yulin shekara ta 2023, har sau 11 ne babban bankin Amurka ya kara kudin ruwa. Kuma hakan ya kan kara darajar kudin musanya na dala. A sabili da haka, darajar kudin musanya, ita ma ta fadada irin wannan “gibin” dake tsakanin yawan GDPn Sin da Amurka.
Muna da yakinin sosai game da bunkasar tattalin arzikin kasar Sin, ba don kwatantawa da na sauran kasashe ba. Mun san cewa, ya kamata tattalin arzikin kasar Sin ya shawo kan wahalhalu da kalubaloli da dama, amma a wadannan shekaru, kasar ta samu ci gaba sosai a yayin da take kokarin shawo kan matsaloli iri-iri. Haye wahalhalu, da shawo kan matsaloli, shi ne abun dake karfafa gwiwarmu ga bunkasar tattalin arzikin kasar Sin. (Murtala Zhang)