Ba sabon labari ba ne cewa Nijeriya ta samu nasarar janyo hankalin kamfanonin kasar Indiya domin zuba hannun jari na biliyoyin dala. Yana da kyau mu dan bi tare da nazartar irin rawar da Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta za ta taka wajen cimma wannan nasarar da ma wasu da dama.
Ba kamar a baya ba, Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu da tawagarsa ta kwararru daga Nijeriya sun samu nasarar aza tubalin ci gaba ta siyasa da tattalin arziki inda suka samu wasu masu zuba jari daga kasar da suka sha alwashin zuba Dala Biliyan 14 a bangaren harkokin bunkasa tattalin arziki.
A karkashin wannan nasara da Nijeriya ta samu akwai abubuwa da dama da suka shafi Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya (NIS). Saboda NIS ita ce hukuma ta farko da ake fara riska da zarar an shigo cikin kasa, da kula da bangaren samar da izinin shigo ga ‘yan kasashen waje (Biza) da kuma sahalewa ga masu shigo cikin kasa, da masu son zama da kuma masu kawo ayyuka a bangarori daban-daban na bunkasar tattalin arziki.
Kazalika, NIS na sanya ido da bibiyar bakin da aka amince su kasance a cikin kasa, da kula da izinin masu gudanar da harkokin kasuwanci, sannan tana da dabarun inganta bayar da Biza ga manyan masu zuba hannun jari, da saukaka wa masu gudanar da kasuwanci harkokinsu da masu ruwa da tsaki da sabbin masu zuba hannun jari inda suke samun aiki mai nagarta cikin sauki daga hukumar. Wannan yakan ba su kwarin guiwa da damar zabar Nijeriya a matsayin kasar da za su zo zuba hannun jarinsu, da tabbatar da shimfidar fuska ga baki, masu zuwa yawon bude ido da sauran fannonin da ke kyautata harkokin tattalin arziki.
Domin kyautata harkokin tattalin arzikin Nijeriya bisa sabon shirin bunkasa arzikin kasa da na yi wa lakabi da “Tinubunomics”, akwai bukatar kara kyautata dangantakar aiki mai ma’ana a tsakanin hukumar NIS, da takwarorinta irin su Hukumar Hana Fasa Kwauri (Kwastam), da Hukumar Kula da Al’amuran Shige da Ficen Teku ta NIMASA, da Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama, da jami’an kiwon lafiya, da na NIPC, da Bankin Ba Da Lamunin Kasuwancin Shige da Fice (NEDIM), da sauran bankunan kasuwanci, da bankunan masana’antu da kuma dokokin da suke gudanar da harkokin zuba jari a Nijeriya, da duba yarjejeniyar da suka shafi aiki da kwararru ‘yan kasashen waje a bangaren kula da bakin waje da kamfanonin da suke musu aiki da dai sauran harkoki da NIS ke zama daya daga cikin masu ruwa da tsaki.
Alllah ya albarkaci Nijeriya da dumbin abubuwan da za a iya zuba musu jari da kuma albarkatun kasa masu tarin yawa. Yanzu haka kasar ta yi nisa wajen kawo gyara mai ma’ana a bangarorin zuba jari da kuma saukaka hanyoyin daukar dawainiyar masu zuwa cikin kasar domin kawo ci gaba.
Bayan haka, ya zama wajibi masu kula da harkokin tattalin arziki su kara maida hankali wajen ganin an rage yawan dogaro da ‘yan kasashen waje ta fuskar gudanar da aikace-aikace da kara ingantawa da muhimmanta amfani da albarkatun kasa da muke da su, da lalubo bakin zaren kara habaka yadda ake mayar da bola zuwa abubuwan amfani. Sannan yana da matukar kyau a kara inganta dokokin harkokin ma’adinai da kuma sanya ido kan filayen da ake bai wa kamfanonin kasashen waje.
Har ila yau, dole ne ma’aikatu da rassansu da sauran hukumomi su tabbatar da yin tsari mai inganci da zai kai ga kyautata tattalin arziki da ba da tasu gudunmawar a wannan fannin. Kana a bi sannu a hankali wajen aiwatar da tsare-tsare da manufofin gwamnati, da rage yawan bata lokaci da tsadar kayayyaki a kasuwannin Nijeriya da ke hana masu zuba jari da dama zama a Nijeriya wanda suke wucewa zuwa kasashen Ghana da sauran kasashen Afirka domin zuba hannun jari ko sayar da kayansu. Akwai bukatar a duba wannan matsalar domin yin kwaskwarima kwarai da gaske.
NIS na da gagarumar rawar da za ta ci gaba da takawa wajen kara janyo kamfanoni domin su zo su zuba hannun jari, da aiki da kwararru, da ‘yan kasuwa, da saukaka kasuwanci da kuma mayar da hankali wajen inganta ayyukan da za su taimaka wajen kara nuna wa masu zuba jari cewar Nijeriya ta cancanta a yi hulda da ita.
CIS James Sunday, shi ne Kwanturolan Hukumar Kula Da Shige Da Fice (NIS) A Jihar Ribas