Auzu billahi minas shaidanir rajim. Bismillahir rahmanir rahim. Allahumma salli ala Sayyidina Muhammadin Alfatihi lima uglika wal-khatimi lima sabaka nasiril hakki bil-hak, wal hadiy ila siradikal mustakiymi wa ala alihi hakka kadrihi wa mikdarihil azim.
Wa radiyallahu an As’habi Rasulillahi (SAW), wala haula wala kuwwata illa billahil Aliyyil Azim.
- Budi Da Cikar Ni’imar Allah Ga Annabi Muhammadu (SAW)
- Budi Da Cikar Ni’imar Allah Ga Annabi Muhammadu (SAW)
Ya himmatas sheikh ihdiriy lana bihazhal mahdari wal-ta’adifiy binazaratin ta’atiy lana biz zafari.
Masu karatu, za mu dan yi waiwaye adon tafiya domin kara daukar darasi a kan karatuttukan da muke yi a kan abin da ya shafi rayuwar fiyayyen halitta, Annabi Muhammad (SAW) musamman a kan abubuwan da suka shafi girmansa, darajojinsa, falalarsa da kuma al’ummarsa (SAW).
Allah (SWT) cikin kudurarsa ya girmama Manzon Allah (SAW) cikin fadi da aikatawa.
Malam Alkadiy Iyad, wanda ya rubuta littafin Asshifa’a, ya yi bayanin cewa sanin darajojin Annabi (SAW) bai buya ba a wajen Malami ko kuma ga duk wanda Allah ya ba shi fahimtar karatu.
Shi ya sa Alhamdu lillah, za a ga duk wani musulmin kirki yana girmama sha’anin Annabi (SAW), yana daraja shi, da an fadi wani abu game da darajojinsa ba zai yi musu ba.
Allah ya kebanci Annabi (SAW) da fifikon abubuwa masu yawan gaske. Komai nasa mai kyau ne da babu irin sa tun daga abin da ya shafi badininsa har zahirinsa. Duk wadannan abubuwan an ruwaito daga Sahabbansa (SAW).
Babu wani wanda zai iya kididdige abubuwan da Allah ya baiwa Manzon Allah (SAW), sai dai kowa ya yi bakin kokarinsa ya gaji ya bari.
Yana daga abin da Allah ya ba shi (SAW) wanda ya zo kuru-kuru a cikin Alkur’ani maigirma, akwai ayoyi da dama da suka nuna girman matsayinsa, da wadanda Allah ya yi ma sa kirari a ciki game da dabi’o’insa da ladabansa. Sannan Allah ya hori sauran bayi su lizimci koyi da halayensa.
Allah ne da kansa ya tsarkake Annabi (SAW) cikinsa da wajensa kuma ya yabe shi a kan haka nan.
Ga duk mai ido da ya yi zamani da Annabi (SAW), ya tabbatar da cewa shi kyakkyawa ne da babu kamarsa.
Hatta Sahabbansa (SAW) su ma sun samu irin wannan albarka, su ma kyawawa ne. Misali, Sayyidina Abubakar (RA) ana ma sa lakabi da Atik, ma’ana mai tataccen fuska. Haka sauran su ma suke.
Annabi (SAW) ya hada kyan jiki da na dabi’a, sannan Allah ya kara karfafa shi da mu’ujizozi (abubuwan mamaki da wani ba zai iya ba), da hujjoji da girmame-girmame da suke a bayyane wanda duk wanda ya yi zamani da shi (SAW) sai da ya gan ta. Ba Sahabbai da suka yi Imani da shi kawai ba, har ma da kafirai duk sun gani.
Wata rana, Abu Jahal ya dauko dutse zai kwada wa Manzon Allah (SAW), sai aka ga ya koma da-baya-da-baya da dutsen a hannu, ‘yan uwansa kafirai suka tambaye shi cewa me ya sa ya dawo alhali ga shi ya je ya same shi a sujadar nan da yake yi bai ya kwada ma sa ba? Sai ya ce musu “Ai wani rakumi na gani ya bude bakinsa kamar zai cinye Makka baki daya ba ma ni ba kawai,”, Manzon Allah (SAW) ya ce “Jibrilu ya gani kuma da ya nemi jefa dutsen da ya gama da shi”. A nan, tabewa ce ta hana Abu Jahal ya musulunta amma ba wai don bai ga mu’ujizozin da ya san cewa Manzon Allah Ma’aiki ne na Allah ba.
Duk wanda ya riski zamani da Annabi (SAW) ya ga wannan girma da darajojin. Sahabbai ma sun ce ko da babu wadannan ma, kallon fuskar Annabi (SAW) kawai ma ya ishe ka abin mamaki bisa yadda take haske da kyalkyali.
Wadanda ba su yi zamani da shi ba, kamar mu da muka zo a baya kenan, muna karanta wadannan darojoji da mu’ujizozi bisa yakini da sakankancewa wanda Tabi’ai suka ruwaito daga Sahabbai, Tabi’ut Tabi’iyna suka ruwaito daga Tabi’ai, su kuma malamai suka rika ruwaitowa daga gare su, abin ya ci gaba a tsakaninsu har ilimin ya zo gare mu, haskensa (SAW) ya kwaranya mana.
Allah (SWT) ya nuna Manzon Allah (SAW) yana da babban girma a wurinsa. A cikin Alkur’ani maigirma, akwai ayoyi masu yawa wadda a sarari suka bayyana kyakkyawan ambaton Manzon Allah, da halayensa, da girmama lamarinsa.
Duk wanda ya riski zamani da Annabi (SAW) ya ga wannan girma da darajojin. Sahabbai ma sun ce ko da babu wadannan ma, kallon fuskar Annabi (SAW) kawai ma ya ishe ka abin mamaki bisa yadda take haske da kyalkyali.
Wadanda ba su yi zamani da shi ba, kamar mu da muka zo a baya kenan, muna karanta wadannan darojoji da mu’ujizozi bisa yakini da sakankancewa wanda Tabi’ai suka ruwaito daga Sahabbai, Tabi’ut Tabi’iyna suka ruwaito daga Tabi’ai, su kuma malamai suka rika ruwaitowa daga gare su, abin ya ci gaba a tsakaninsu har ilimin ya zo gare mu, haskensa (SAW) ya kwaranya mana.
Daga cikin abin da ya zo da haka da yi ma sa kirari da bayyana kyawawan abubuwan da suka shafi Annabi (SAW) ita ce ayar nan ta “Lakad ja’akum”.
Allah (SWT) ya ce, “Hakika (wallahi) wani Babban Ma’aiki ya zo muku daga cikinku, ya fi ku damuwa a kan abin da ke wahalar da ku, mai kwadayin shiriya ne a gare ku, a wurin Muminai kuma mai tsananin tausayi ne da jinkai.”
Wannan aya tana nuna yadda Annabi (SAW) ya ke son al’ummarsa, duk abin da zai wahalar da su, yakan damu kwarai da gaske a kai. Misali, iyaye idan dansu ba shi da lafiya sukan fi shi damuwa har su rika jin ina ma da rashin lafiyar dan za ta dawo jikinsu shi ya huta, saboda tausayi. To haka mu al’ummar Annabi (SAW) muke a wurinsa.
Allah (SWT) Yana yabon Annabi (SAW) ne a cikin ayar tare da buga misali kan kyawawan halayensa masu girma.
Malam Samarkanda, masanin fikihu mai bin Maz’habar Hanafiyya kuma Sufi (mai gyaran zuciya) ya ce, “wani sashe (na malamai) suna karanta ayar da ‘min anfasikum’ ba ‘min anfusikum’ ba”. Kuma watakila ana cewa haka Annabi (SAW) yake karantawa. Amma Kuma a karatun mafi akasarin Sahabbai (RA), da ruwayoyin kira’o’in nan guda 10 ana karantawa ne da ‘min anfusikum’.
Malam Alkadiy Abul-Fadli, masanin Hadisi ya ce ma’anar ‘min anfusikum’, “Allah ya sanar da Muminai cewa Manzon Allah ya zo daga cikinsu, ko Larabawa ne aka fada wa haka, ko mutanen Makka ko kum dukkan mutane ne ake nufi”.
Abin da ya sa Malaman Tafsiri suke da wannan fahimtar shi ne kowanne a cikin hudun nan akwai ayar da ta nuna da shi ake kuma babu yadda za ce wata ayar ta fi wata, saboda haka shi Malamin Tafsiri zai iya tafiya a kan ayar da ya dauka.
Wadanda suka tafi a kan cewa ayar tana nuna da Muminai ake, sun dogara ne da ayar cikin Suratu Ali Imran, “Hakika (wallahi) Allah ya yi baiwa ga Muminai da ya aiko wani Babban Manzo daga cikinsu, (Manzon nan) yana karanta musu ayoyin Allah, yana tsarkake su kuma yana sanar da su rubutu da ilmi (ko yana karanta musu Alkur’ani da Hadisi ko yana sanar da su Shari’a da Hakika, (duk dai akwai maganganu a kai), ko da muminan nan sun zamo suna cikin neman shiriya mabayyana”.
A cikin wannan ayar, Allah ya nuna da Muminai ake. Allah ya yi wa Muminai baiwa da ni’imomi kala-kala, amma babbar kyauta da ni’imar da Allah ya yi musu babu kamar aiko Annabi (SAW) daga cikinsu.
Ko kuma a’a, Larabawa ake nufi. Domin Annabi (SAW) Balarabe ne, Alkur’aninmu da Larabci aka yi shi, maganar ‘yan gidan Aljanna Larabci ne, al’adar Addninmu na Musulunci al’ada ce ta Larabawa.
Don haka duk Musulmi Balarabe ne, domin kowane yare mutum yake, idan zai karanta Alkur’ani da Larabci zai yi. Kan haka sai muka zamo dukkanmu kamar Larabawa.
Saboda haka sai wasu suka fahimci cewa ayar tana nufin Larabawa ne Allah yake magana da su, yake musu gorin cewa ya ishe su daraja mafi girma samun Annabi (SAW) a cikinsu.
Ayar da ta zo a cikin Suratul Jumu’ati ta karfafa wannan, “Shi (Allah) ne wannan da ya aiko a cikin Larabawa (ummiyyai, ma’ana wanda ba su yin rubutu, ba su yin karatu; komai nasu haddacewa ne) Ma’aiki daga cikinsu da yake karanta musu ayoyin Allah, yana tsarkake su, yana karanta musu ayoyin Allah da hikimah, koda yake (Larabawa kafin zuwan Manzon Allah) suna cikin bata mai girma mabayyani”.
Ko kuma ayar ta Lakad ja’akum wurin “min anfusikum” tana nufin Allah ya aiko Annabi (SAW) ne daga cikin Mutanen Makka. Saboda kalmar “Ummiyyu” a wannan fahimtar, tana nufin “Ummul Kura”, wato Garin Makka. Ko Kuma su mutanen Makka ‘yan kasuwa ne da babu ruwansu da rubutu da karatu, kasuwancin kawai suka sanya a gaba, shi ya sa ake ce musu “Ummiyyai”.