ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, July 26, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Budi Da Cikar Ni’imar Allah Ga Annabi Muhammadu (SAW)

by Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
3 years ago
Annabi

Jama’a assalamu alaikum. Har yanzu dai muna nan cikin darasinmu da muka faro a makon da ya gabata wanda muke waiwaye a kan karatun da muka taba yi dangane da budi da cikar daraja da ni’imar da Allah ya yi ga Manzon Allah (SAW), musamman daga Suratul Fat’hi.

Kamar yadda muka yi bayani a makon da ya gabata, Allah mai girma da daukaka (a farkon surar) ya fara ne da sanar da Annabi (SAW) abin da ya hukunta a gare shi na daga hukunci mabayyani cewa Allah ya dora shi a kan makiyansa.

  • Ba Zan yi Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ba, Cewar Dikko Radda
  • Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka Na Kara Haifar Da Da Mai Ido

Allah ya bayyana addinin Annabi (SAW) ya cika ko ina, yau ina su Abu Jahli? Allah ya rinjayar da Annabi a kan makiyansa da daukakar kalmar Manzon Allah (SAW) da Shari’arsa.

ADVERTISEMENT

Duk wadannan sun tatttaru ne a cikin fadin Allah (farkon surar) cewa shi Annabi (SAW) abin gafartawa ne a gare shi (duk abin da ya aikata na barin tarku aula), ba wanda za a rika ne da wani laifi ba, ba wani abu da zai yi nan gaba kuma a ce an rike shi da laifi.

Wani sashe na malamai ya ce, wannan yana nufin an gafarta masa ne (SAW) idan da ma akwai wani abu da ya kasance (na laifi) da abin da ma bai kasance ba da zai zo nan gaba, Allah ya gafarta masa. Sai mu lura a nan, duk da Allah ya ba Manzon Allah (SAW) garanti cewa an yafe masa (abin da ya yi a baya da wanda zai yi a gaba) amma Manzon Allah bai aikata wani abin assha ba. Shi ma Manzon Allah haka ya din ga yi wa wasu Sahabbansa garanti, yana fadin wane dan aljanna ne, wane da aljanna ne. Kuma su ma ba a ga suna aikata wani abin assha ba. Manzon Allah (SAW) ya ce duk ‘Yan Badar (wadanda suka halarci yakin Badar) Allah ya gafarta musu, duk abin da suka aikata ba za su shiga wuta ba, to kuma ba a ga wani Dan Badar ya yi shirka da Allah ko ya aikata wani laifi da za a iya cewa na assha ba ne.

LABARAI MASU NASABA

Falalar Yawaita Istigifari (2)

Falalar Salatut Tasbihi

Malamai sun ci gaba da bayanin cewa abin da ayar (ta farkon surar) take nufi, shi ne (ya Rasulallahi SAW) kai abin gafartawa ne. Malam Makki ya ce Allah ya sanya baiwa sababi ce ta gafara, duka da baiwar da gafarar daga Allah ne wanda babu abin bautawa da gaskiya sai shi. Bayan baiwa, darajantawa ne Allah ya ba Annabinsa. Sannan Allah ya ce zai cika ni’imarsa ga Annabi (SAW). Malamai suka ce meye cikar ni’ima ga Annabi (SAW) da Allah yake nufi? Suka ce ita ce kaskanta makiyansa (komai karfinsu na kudi da mulki) su dawo a karkashinsa. Kila kuma malamai suka ce cikar ni’imar tana nufin Allah zai bude masa Makka (Fatahu Makkata), ya so shiga sun hana shi sun ce sai dai ya dawo badi, to bari wata rana garin zai zama nasa, wand ya ga dama zai bar shi ya zauna a garin; wanda bai ga dama ba kuma ya kore shi kuma ya koru (SAW). Tana kuma nufin Allah zai bude wa Manzon Allah (SAW) Da’ifa. Kila kuma ma’anar cika ni’ima ga Manzon Allah (SAW) tana nufin Allah zai daga ambatonsa a nan duniya. Ba yanda za a yi ambaton Manzon Allah ya gushe, ba wanda yau a duniya zai ce bai san ambatonsa ba. Ga shi nan duk kiran sallah biyar sai an fadi sunansa kuma da karfi cikin daga murya, bayan sauran wuraren da ake ambatonsa kamar su tahiya da sauransu. In dai za a ambaci Ubangiji to sai an hada da Bawansa (Annabi SAW).

Allah zai taimake ka, Allah zai gafarta maka (ya Rasulallah SAW). Sai Allah ya sanar da shi (SAW) cikar ni’imarsa a gare shi ta hanyar kaskantar masa da girman makiyinsa, da bude masa mafi soyuwar garuruwa a gare shi (Makka), duk Allah ya bude masa. Haka nan Allah ya nuna masa zai bude masa Hira da Sham da Mada’in da Rum duk gabadaya ya fada wa Sahabbansa. Allah zai daukaka ambatonsa da shiryar da shi tafarki madaidaic, tafarkin da zai kai (mutum) zuwa Aljanna da arzikin lahira da taimakonsa, taimakon da ya zama mabuwayi da baiwar Allah ga al’ummarsa. Bayan ni’imar a kan Annabi (SAW), Allah Ta’ala ya kuma faranta wa Annabi rai a cikin al’ummarsa Muminai wanda ya natsar da zuciyarsu da natsuwa wanda Allah ya sanya a cikin zukatansu. Duk Mumini sai ka ga zuciyarsa a natse, za ka ga yana yin ayyukansa cikin hankali da natsuwa, amma duk wanda ba haka ba, sai ka gan shi a cikin tashin hankali, ko karatu zai yi sai ka ji yana yi a cikin tashin hankali kai ka ce sakon da yake isarwa da fada aka aiko, misalin irin wannan kamar kare ne, in ka bige shi ko ka bi shi da gudu zai yi haki; haka nan idan ka kyale shi yana hutawa duk dai za ka ga yana haki, Allah ya kiyaye mu. Mutum ya zamo yana cikin natsuwa.

Allah ya kuma yi wa (Muminan) bushara da abin da yake gare su a wurin Ubangiji. Duk Musulmi in dai ya yi imani (La’ila ha illallahu Muhammadur Rasulullah SAW), sauran abubuwa suna da sauki, zai samu Rahamar Allah. Komai laifin da Musulmi zai yi idan ya mutu ba za a ce yana wuta ba, sai dai a ce ya tafi Mashi’ar Allah, idan Allah ya ga dama ya azabtar da shi, idan kuma ya ga dama ya sa shi a rahama. Allah yana cewa mece ce ribar da zai ci idan ya yi muku azaba in dai kuka yi imani kuka yi godiya? Mutum ya yi imani da Allah iya kokarinsa, Allah Ta’ala zai gafarta masa, ya yarda da Allah; ya san Allah alheri ne ya yi nufi da shi, ya sa dadi a zuciyarsa; ba ya dinga yi wa Allah mummunan zato ba. Ai ka ga ma a karatunmu na baya, Allah ya ce yana mana bushara muna da wata ajiya a wurinsa, ajiyar shi ne Annabi Muhammadu (SAW). Kowane Musulmi ya yi bishara, ya san bayan imaninsa na Musulunci, bayan ibadarsa, yana da wata ajiya a Bankin Allah, shi ne Annabi Muhammadu (SAW), idan ka zama kana da Annabi (SAW) a lahira wannan babban alheri ne; ya ishe ka.

Allah ya ce wa Annabi (SAW) gaya musu, ku yi farin ciki da falalar Allah da rahamarsa (fiye da aikinmu, kar mutum ya ga aikinsa ne zai ba shi abu a wurin Allah, ba kuma wai kar mu ki yin aikin ba, a’a, mu yi aiki tukuru, amma mu san mun dogara ne da falalar Allah da rahamarsa domin duk abin da muka yi na ibada idan babu falalar Allah da rahamarsa banza ne.

Wani mutum ya zo wurin Shehu Tijjani Abul Abbasi (RTA) ya ce, “Shehu Allah ya jarrabe ni da wani laifi; na yi-na yi in bari na kasa, yi mun addu’a Allah ya raba ni da shi”. Shehu Tijjani ya ce masa “je ka Allah ya karbe ka a bisa kowane hali”, sai mutumin ya ce “a’a ni dai ka yi mun addu’a in bari”. Shehu Tijjani ya ce masa “to wai kai a zatonka in ka bari (aikata laifi) din, idan ba zai karbe ka; karbar ka zai yi? Ka je Allah ya karbe ka kawai”. Kila Allah ya haska wa Waliy (Shehu) ya ga mutumin nan ba zai iya barin aikata laifin ba, to ka ga gara ya roka masa Allah a cikin falalarsa ya yafe masa, Allah ya shigar da shi Aljanna. Mu dogara da falalar Allah, mu yi ta aiki, amma mu san falalar Allah da rahamarsa su ne babban abin da muke dogara da shi, wannan kuma shi ne Annabi (SAW).

 Allah duk ya yi mana busharori na abin da muke da shi a wajensa. Da samun babban rabon al’ummarsa (SAW) mai girma, da yi mana rangwame, ba wai ba mu da laifi ba ne, a’a, muna da laifi zunkur, waye zai ce ba shi da laifi in dai ba Annabi ba? Waye wannan da bai taba laifi ba in ba Manzon Allah (SAW) da wanda Allah ya kiyaye ba? Amma da laifin da komai sai Allah ya gafarta ma, ka san kana da laifin kuma ka kankan da kai da kwadayin Rahamar Allah. Allah ya ce yana nan a wurin mutanen da zuciyarsu ta karye, sun san sun saba masa, amma zuciyarsu sai ta karye domin sun san suna da Ubangiji. Babban laifi dai shi ne Allah ya jarrabi mutum da kekashewar zuciya ya rika ganin laifin ma banza ne, amma wanda zai aikata laifi ya ji zuciyarsa tana kuka, to wannan Allah zai gafarta masa gabakidaya. Amma duk wanda zuciyarsa za ta kekashe ya ga laifin da ya yi ma ba laifi ba ne, to wannan ya shiga hadari. Allah mai sitarta zunubin al’ummar Annabi (SAW) ne da halakar da makiyan Manzon Allah a duniya da lahira da la’antarsu da nesantar da su daga Rahamarsa. Duk wannan falala ce da Allah ya yi wa Annabi (SAW). Duk wanda yake kin Annabi zai gamu da mummunar makoma.

Annabi
Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
+ postsBio
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Yawaita Istigifari (2)
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Salatut Tasbihi
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW
  • Shehu Ismaila Umar Mai Diwani
    https://hausa.leadership.ng/author/shehu-ismaila-umar-mai-diwani/
    Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

MASU ALAKA

Falalar Yawaita Istigifari (2)
Dausayin Musulunci

Falalar Yawaita Istigifari (2)

July 24, 2026
Falalar Salatut Tasbihi
Dausayin Musulunci

Falalar Salatut Tasbihi

July 17, 2026
Matsalar Tsaro: Gwamnatin Tarayya Ta Nemi Taimakon Ƙasashen Waje
Dausayin Musulunci

Falalar Yawaita Salati Ga Annabi Muhammad SAW

July 3, 2026
Next Post
Halin Da Muke Ciki A Nijar – Yusuf Buzu

Halin Da Muke Ciki A Nijar – Yusuf Buzu

LABARAI MASU NASABA

Dauda Dauda Lawal Ya Sha Alwashin Farfaɗo Da Masana’antar Yadi Ta Zamfara

Dauda Dauda Lawal Ya Sha Alwashin Farfaɗo Da Masana’antar Yadi Ta Zamfara

July 26, 2026
Gwamna Uba Sani Ya Ƙaddamar Da Rabon Taki Kyauta Ga Manoma 150,000  A Kaduna

Gwamna Uba Sani Ya Ƙaddamar Da Rabon Taki Kyauta Ga Manoma 150,000 A Kaduna

July 26, 2026
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

Birtaniya Ta Yaba Wa Tinubu Kan Sauye-sauyen Tattalin Arziki

July 25, 2026
Ofishin Jakadancin Sin A Nijeriya Ya Shirya Taron Murnar Cika Shekaru 99 Da Kafuwar Rundunar PLA Ta Sin

Ofishin Jakadancin Sin A Nijeriya Ya Shirya Taron Murnar Cika Shekaru 99 Da Kafuwar Rundunar PLA Ta Sin

July 25, 2026
Sabon Rahoton Bankin Duniya Ya Yaba Da Yadda Tattalin Arzkin Nijeriya Ke Bunkasa

Sabon Rahoton Bankin Duniya Ya Yaba Da Yadda Tattalin Arzkin Nijeriya Ke Bunkasa

July 25, 2026
Farfesa Dr. Otto Heinrich Herzog: Sin Tana Da Tsari Mai Kyau Na Aiwatar Da Dabarun Ci Gaba

Farfesa Dr. Otto Heinrich Herzog: Sin Tana Da Tsari Mai Kyau Na Aiwatar Da Dabarun Ci Gaba

July 25, 2026
Yadda Ake Faten Dankalin Turawa Da Kaza

Yadda Ake Faten Dankalin Turawa Da Kaza

July 25, 2026
An Watsa Shirin Talabijin Mai Taken “Yiwu Ta Duniya –Yadda Xi Jinping Ke Kulawa Da Jagorantar Ci Gaban Yiwu”

An Watsa Shirin Talabijin Mai Taken “Yiwu Ta Duniya –Yadda Xi Jinping Ke Kulawa Da Jagorantar Ci Gaban Yiwu”

July 25, 2026
Baya Ga “Sanyi Irin Na Sin”, Akwai Wasu Abubuwa Da Yawa Da Masu Yawon Bude Ido Na Turai Ke Sha’awa Kan Kasar

Baya Ga “Sanyi Irin Na Sin”, Akwai Wasu Abubuwa Da Yawa Da Masu Yawon Bude Ido Na Turai Ke Sha’awa Kan Kasar

July 25, 2026
Rodri Ya Amince da Tayin Komawa Real Madrid

Rodri Ya Amince da Tayin Komawa Real Madrid

July 25, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.