INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN!
Allah ya yi wa mahaifiyar limamin masallacin Annabi (SAW) da ke Madina, Sheikh Abdurrahman Huzaify, rasuwa

Sheikh Abdurrahman Huzaify, babban Malamin Musulunci ne makarancin Al-qur’ani mai girma kuma guda cikin masu jagorantar Sallah a masallacin Madina da ke kasar Saudiyya.
Shafin Haramain Sharifaini ne ya sanar da rasuwar mahaifiyar babban malamin a yammacin yau Juma’a ranar Arfat 1443/2022 kuma daren idin babbar Sallah.
Muna Addu’ar Allah ya gafarta mata, ya kyauta bayanta, ya kyauta tamu bayan ta su, Amin.