Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya jajanta wa ‘yan uwa da iyalansa bisa rasuwar ‘yar uwarsa, Hajiya Laraba Dauda wadda ta rasu ta bar ‘ya’ya da jikoki da dama.
Kamar yadda wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu ya fitar, marigayiyar ta rasu ta bar ‘yan uwa da dama, ciki har da Malam Mamman Daura, wanda yayan shugaban kasa ne wanda ya je Daura domin jajantawa ‘yan uwa rasuwarta.
- Li Keqiang: Shigar Sin WTO Ta Haifar Da Ci Gaba Ga Sassa Daban Daban
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 9 A Musayar Wuta A Kaduna
Shugaba Buhari ya bayyana marigayiya Laraba a matsayin “mahaifiya mai kulawa, ma’abociyar rayuwa da hakuri, mai matukar kishin rayuwar danginta.”
”Rasuwarta abin bakin ciki ne, amma Allah ne Mafi sani. Ina mika ta’aziyyata ga duk iyalan da ta bari.
“Allah ya jikanta,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp