• English
  • Business News
Wednesday, October 15, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Almundahana: LP Ta Nada Sanata Ireti Kingibe Domin Binciken Tsohon Shugaban Jam’iyyar

Ta bai wa Tsohon Shugaban Sa'o'i 48 ya kare kansa

by Sulaiman
5 months ago
LP

Majalisar zartaswa ta Jam’iyar Adawa ta Labour party (LP) a karkashin jagorancin Sanata Nenadi Usman da Sakataren Jam’iyar, Sanata Darlington Nwokwocha, ta kafa wani kwamitin horo, karkashin jagorancin Sanata Ireti Kingibe da wasu mambobi hudu domin su binciki Almundahana da zagon Kasa Ga Jam’iyar Wanda ake zargin tsohon Shugaban Jam’iyar Julius Abure da aikatawa.

Hakan ya biyon bayan wani taron manema labarai, Wanda Shugaban Jam’iyar (mai rikon kwarya) na Kasa, Sanata Nenadi Usman ta yi a Abuja.

  • Zamfara Ta Haɗa Gwiwa Da Oracle A Landan Don Bunƙasa Fasahar Matasa A Jiharta 

Shugaba Xi Ya Isa Moscow Domin Fara Ziyarar Aiki A Rasha

An dai bai wa kwamitin wa’adin sati uku domin su gabatar da rahoton su. Ita dai Sanata Ireti Wanda ke wakiltar Birnin tarraya Abuja, itace za ta Shugabanci kwamitin sai kuma aka nada Peter Ameh a matsayin sakataren kwamitin.

LABARAI MASU NASABA

Da Ɗumi-ɗumi: Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ya Ƙara Raguwa Zuwa Kashi 18.02%

Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Dajin Taraba

Har ila yau, kwamitin zai bada shawara akan hukuncin da Jam’iyar za ta dauka Idan har aka sami wanda ake zargi da laifin almundahana da kuma zagon Kasa ga LP a lokacin da yake Shugabantar jam’iyar.

Sanata Usman ta zargi Abure da mukarrabansa da aikata laifufuka dake janyo rabuwar Kai ga ‘ya’yan Jamiyar tare da batanci da haddasa rikici.

Sanata Usman ta Kara da cewa, Abure yana aikata laifufuka wanda suke kalubalantar mutunci Jam’iyar da kuma yin karo da manufofin dimokuradiyya. Don haka, majalisar zartaswa ta Jam’iyar ta dauki matakin kaddamar da bincike kan wannan munanan halayya.

Bugu da Kari Sanata Nenadi Usman tace majalisar zantaswa na Jamiyar Labour bayan dogon nazari akan hukuncin da kotun koli ta Kasa ta yi na ranar 4 ga watan Afrilun 2025, Jam’iyar ta nuna matukar damuwarta akan Yadda Julius Abure yake amfani da sunan shi a matsayin Shugaban Jam’iyar bayan wa’adin jagorancin shi ya cika.

Ta ce, abubuwan da Julius Abure yake yi ya sabawa dokar Kasa kuma ya ci mutuncin Jamiyar. A sabo da haka ne tace kundin tsarin mulkin Jamiyar na shekarar  2019 (Wanda aka yi wa Kwaskwarima) ya Basu damar daukan kwararan matakai da hukunci akan Julius Abure.

Daga bisani, Sanata Nenadi Usman ta nuna rashin amincewarta akan Yadda Julius Abure yake cin mutunci jagoran jam’iyar Labour na Kasa, Peter Obi da Gwamna Alex Otti. Tace Abure da mukarabansa wadanda wa’adinsu ya kare, basu da hurumin magana da yawun Jam’iyar kuma baza su iya dakatar da Gwamnan ba ko wani mamban Jamiyar.

Ta kuma shaidawa ‘Yan Nijeriya cewa, Jam’iyar ta sanar da Hukumar Zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) akan shirye-shiryenta na gudanar da zabuka a matakai daban-daban tare da gudanar da babban taron Jam’iyar na kasa.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

sallah
Manyan Labarai

Da Ɗumi-ɗumi: Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ya Ƙara Raguwa Zuwa Kashi 18.02%

October 15, 2025
Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Dajin Taraba
Labarai

Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Dajin Taraba

October 15, 2025
Yajin Aikin: Ɗalibai Sun Bai Wa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana 7 Su Warware Rikicinsu
Labarai

Yajin Aikin: Ɗalibai Sun Bai Wa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana 7 Su Warware Rikicinsu

October 15, 2025
Next Post
Tinubu Ya Dawo Abuja Bayan Halartar Taron Sauyin Yanayi A Dubai

Tinubu Ya Kai Ziyarar Aiki Jihar Anambra

LABARAI MASU NASABA

Da Ɗumi-ɗumi: Ladan Bosso Ya Ajiye Aikin Horar Da Barau Fc 

Da Ɗumi-ɗumi: Ladan Bosso Ya Ajiye Aikin Horar Da Barau Fc 

October 15, 2025
An Bude Bikin Baje Kolin Kasuwanci Na Kasa Da Kasa Na 138 A Guangzhou

An Bude Bikin Baje Kolin Kasuwanci Na Kasa Da Kasa Na 138 A Guangzhou

October 15, 2025
sallah

Da Ɗumi-ɗumi: Hauhawar Farashin Kayayyaki A Nijeriya Ya Ƙara Raguwa Zuwa Kashi 18.02%

October 15, 2025
Mujallar “Qiushi” Za Ta Wallafa Muhimmiyar Kasidar Shugaba Xi Jinping Kan Muhimman Shawarwari Hudu Da Ya Gabatar

Mujallar “Qiushi” Za Ta Wallafa Muhimmiyar Kasidar Shugaba Xi Jinping Kan Muhimman Shawarwari Hudu Da Ya Gabatar

October 15, 2025
Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Dajin Taraba

Sojoji Sun Fatattaki ‘Yan Ta’adda A Dajin Taraba

October 15, 2025
Xi Jinping Ya Taya Patrick Herminie Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Seychelles

Xi Jinping Ya Taya Patrick Herminie Murnar Lashe Zaben Shugaban Kasar Seychelles

October 15, 2025
Yajin Aikin: Ɗalibai Sun Bai Wa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana 7 Su Warware Rikicinsu

Yajin Aikin: Ɗalibai Sun Bai Wa ASUU Da Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwana 7 Su Warware Rikicinsu

October 15, 2025
Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP

Gwamna Diri Da ’Yan Majalisa 23 Na Bayelsa Sun Fice Daga PDP

October 15, 2025
Shugaban Kasa Yana Bibiyar Zanga-zangar Matsin Rayuwa – Minista

2027: Babu Ɗan Siyasar Da Zai Iya Ƙalubalantar Tinubu — Fadar Shugaban Ƙasa

October 15, 2025
Tinubu Ya Nemi Jihohi Su Dakatar Da Karbar Haraji A Kan Masu Safarar Kayan Abinci

Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba Barazana Ce Ga Tsaro A Yammacin Afirka – Tinubu

October 15, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.