Mazauna kauyuka da dama a karamar hukumar Kebbe da ke jihar Sokoto sun nuna damuwarsu kan yadda ‘yan bindiga ke ci gaba da kai musu hare-hare, lamarin da ya janyo kashe-kashe, sace-sacen mutane, da sanya fargaba a cikin zukatan jama’ar yankin.
Da suke jawabi a taron manema labarai a ranar Asabar din da ta gabata, shugabannin al’ummomin karkashin jagorancin Alhaji Adamu Haruna daga garin Kebbe, sun bayyana taɓarɓarewar tsaro a matsayin abin takaici, inda suka yi gargadin cewa, janye hannun gwamnati na iya sa jama’a su fara ɗaukar matakan kare kansu.
- Firaministan Pakistan: Shugaba Xi Jinping Shugaba Ne Mai Hangen Nesa
- Kokarin Da ‘Yan Wasan Nijeriya Suka Yi Wajen Lashe Kyautar Ballon d’Or
“Rayuwarmu na cikin haɗari, sun kwashe dukiyoyinmu, dabbobinmu, kuma yanzu sun fara sace mutane,” in ji Haruna.
Ya kara da cewa, “Ba a bar mu mun yi noma ba, kuma ana kwace mana kayanmu, Haƙurin mutane ya fara kaiwa bango.”
“Mutane suna rayuwa cikin tsoro, waɗannan miyagu suna barazanar hana mu girbin amfanin gonakinmu.
“Akwai wata ƙungiya da ake kira Lakurawa da kowa ke tsoro – karfinsu a yankin yana ƙaruwa.” Haruna ya ƙara da cewa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp