Al’ummar Yarabawa a Jihar Kano sun gudanar da taron addu’o’i daga mabiya addinai daban-daban a ranar Lahadin da ta gabata don neman zaman lafiya, ci gaba da kuma daidaita harkokin siyasa a kasar nan.
Jagoran taron, Malam Abdulsam Abdullateef, ya shaidawa manema labarai cewa jihar Kano ta zama gida na biyu ga wadanda ba ‘yan asalin jihar ba, don haka taron ya ja hankalin malamai da mabiyan kungiyoyi da dama.
- Zabe: Kotun Kano Ta Kwace Kujerar Datti Ta Baiwa Iliyasu Kwankwaso
- Kotun Sauraren Kararrakin Zabe Dan Majalisar Wakilai A Kano Ta Tabbatar Da Nasarar Kofa
Abdullateef, tsohon mai baiwa tsohon gwamnan jihar Kano shawara kan hulda tsakanin al’umman na, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya ce salon siyasar Kwankwaso ne tabbatar da hadin kai.
Haɗin kai, in ji shi, ya share fage ga waɗanda ba ƴan asalin ƙasar ba, su kasance cikin tsarin siyasar da ya zayyana a matsayin ɗabi’ar dimokuradiyya a jihar Kano.
Ya ce Yarbawa a jihar Kano suna goyon bayan gwamnati mai ci a yanzu ta, Abba Yusuf, a kokarinta na kwato hakkin wadanda aka zalunta.
“A cikin watanni takwas kafin zaben 2023, Kwankwaso, shugaban NNPP, ya sake karfafa jam’iyyar kuma ta lashe dukkan kujerun majalisun tarayya da na jiha da kuma kujerar gwamna,” in ji Abdullateef.
Ya yaba wa Gwamna Yusuf bisa yadda ya kiyaye ka’idoji, akidu da dabarun salon “Kwankwasiyya” (salon shugabancin Kwankwaso) wanda a cewarsa, ya fara inganta tsarin mulki a jihar Kano.
“A cikin kwanaki 100 da Gwamna Yusuf ya yi yana mulki, Jihar Kano ta samu ingantattun ababen more rayuwa.
“Asibitoci sun fara aiki sosai kuma titunan Kano sun yi haske sosai; fizge wayan da ya zama bala’in garin ma ya kau.
“Fiye da dalibai 1,000 ne suka ci gajiyar tallafin karatu a gida da waje, yayin da aka dawo da makarantun da gwamnatin da ta gabata ta yi watsi da su,” in ji Abdullateef.