Jarumar Fina-finan Kannywood, Amal Umar ta gurfana a gaban kotun majistare mai lamba 24 da ke unguwar Gyadi-Gyadi a cikin birnin Kano, bisa zargin yunkurin bai wa jami’in tsaro cin hanci.
Ana zargin jarumar da yunkurin bada cin hancin kudi har Naira 250,000 ga wani jami’in ‘yansanda mai suna ASP Salisu Bujama na rundunar ‘yan sandan Nijeriya, hedikwatar shiyya ta daya a jihar Kano.
- Yunkurin Yin Katsa Landan Ba Zai Dakile Ci Gaban Yankin HK Ba
- Ranar Tunawa Da Jarumai: Gwamnatin Kano Za Ta Kafa Gidauniyar Tallafawa Iyalan Sojojin Da suka Rasu
A cewar mai gabatar da kara, Amal ta bayar da cin hancin ne da nufin a dakatar da binciken ‘yansanda kan zargin karkatar da kudade da saurayin jarumar, mai suna Ramadan Inuwa yayi a wata harka ta kasuwanci.
Laifin da ake zargin jarumar ta Kannywood da aikatawa, ya sabawa sashe na 118 na kundin laifuffuka, wanda ya haramta bayarwa da karbar cin hanci ga jami’an tsaro.