Wata sabuwar matar aure mai suna Misis Rukayat Musa da surukanta biyu da aka yi garkuwa da su a gidansu da ke titin sarki a Ilorin sun kubuta.
Rahotanni sun ce sun samu ‘yancinsu ne bayan an biya su kudin fansa Naira miliyan bakwai.
- Dan Sanda Ya Shiga Hannu Kan Yunkurin Kashe Abokin Aikinsa A Kaduna
- Matawalle Bai Saci Kudin Jihar Zamfara Ba — Anas Kaura
Wadanda suka sace su sun bukaci Naira miliyan 50.
Rahotanni sun ce an sako Rukayat da wadanda aka sace, Hafsat da Aliyah, da sanyin safiyar Lahadi.
An yi garkuwa da su ne da sanyin safiyar Alhamis lokacin da ‘yan bindigar suka kai farmaki gidan ma’auratan da ke unguwar Oniyangi da ke kan titin sarki, Ilorin.
A lokacin da lamarin ya faru, mijin nata, Musa, ya tsere bayan wadanda suka yi garkuwa da su sun samu shiga gidan ma’auratan da ke unguwar Alaya.
Daga baya masu garkuwa da mutanen sun tuntubi iyalan inda suka bukaci a biya su kudin fansa naira miliyan 50 kafin a sako matan uku.
Rahotanni sun ce sun yi gargadin cewa dole ne a cika sharuddan nan da karshen mako, inda suka yi barazanar kashe matan.
Rukayat ta fito ne daga harabar Gbodofu da ke kusa da yankin Balogun Fulani a Ilorin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Okasanmi Ajayi, ya ce bai san da faruwar lamarin ba, ya kara da cewa watakila ba a kai rahoton lamarin ba.
“Ban san faruwar lamarin ba, babu wanda ya gaya min labarin sace sabuwar amaryar.
Amma wani dan uwa ga amaryar da bai so a ambaci sunansa ba, ya ce an sako matan uku ne da sanyin safiyar Lahadi.
“Sun isa Ilorin ne suka kira mu da misalin karfe 2 na ranar Lahadi amma ba a sake su ba kyauta.
“Iyalan sun biya kudin fansa Naira miliyan bakwai.
“Ba za mu iya tara kudin da suka kai haka ba, sai muka yi kuka muna rokonsu kafin su karbi Naira miliyan bakwai da muka tara”.
Ya ce “An kai matan uku asibiti nan take domin yi musu magani. Har yanzu suna asibiti.”