Gwamnatin tarayya ta kafa gidauniyar bada agajin gaggawa domin rage radadin annoba da ke afkuwa ba zata kamar ambaliyar ruwa.
Ministan Kudi kuma Ministan Tattalin Arziki, Wale Edun ne ya bayyana hakan ga manema labarai a fadar gwamnati, ranar Litinin bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya, wanda shugaban kasa Bola Tinubu ya jagoranta.
- Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Taraba Ta Buƙaci Mazauna Kwarin Kogin Benuwe Su Ƙaurace Wa Yankin
- Libya Ƙasar Da Man Fetur Ya Fi Arha A AfrikaÂ
A cewar ministan, tabbas za a iya samun annoba a wannan zamani na sauyin yanayi ko da kuwa an dauki matakan rigakafin da suka da ce.
Ya jaddada muhimmancin hada kudade daga sassa daban-daban da kuma shirye-shiryen magance matsalolin gaggawa.
Ya bayyana cewa, wannan kudiri na da nufin aiwatar da shawarwarin kwamitin ya ki da annoba, kamar ambaliyar ruwa.
Bugu da kari, Ministan Muhalli, Joseph Ustev, ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya ta kafa wani kwamiti da zai tantance dukkan madatsun ruwa a kasar.