Akalla kashi 80 cikin 100 na dabbobin da aka ajiye a gidan ajiye namun daji (Zoo) na Sanda Kyari da ke Maiduguri sun mutu sakamakon ballewar madatsar ruwa ta Alau da ke karamar hukumar Konduga a jihar a ranar Litinin.
Babban Manajan Gidan Zoo din a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Maiduguri, ya kara da cewa, wasu daga cikin miyagun dabbobi irin su kada da macizai, duk ambaliyar ta watsa su cikin al’umma, don haka, ya gargadi al’umma da su dauki matakan da suka dace don gujewa dabbobin.
- Tinubu Ya Bayar Da Umarnin Gaggauta Kwashe Waɗanda Ambaliya Ta Ɗaiɗaita A Maiduguri
- Tallafi: Tinubu Ya Nuna Son Rai Wajen Raba Kayan Abinci – Kwankwaso
A halin da ake ciki, Jami’ar Maiduguri da Jami’ar Jihar Borno sun rufe makarantun sakamakon ambaliyar da ta afku a Maiduguri inda ta mamaye al’ummomi da dama.
Mukaddashiyar babbar mataimakiyar magatakardar Jami’ar BOSU, Fatima Muhammad Audu, ta ce, dole ne cibiyar ta bi umarnin ma’aikatar ilimi, kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire ta jihar Borno na rufe jami’ar daga ranar Talata 10 ga Satumba zuwa Litinin 16 ga Satumba. 2024.